Yajin kuli kuli

MJ's Kitchen
MJ's Kitchen @mjrena
Lagos

Wanan shine recipe din MJ's kitchen na musamman🤗, masu neman abin hadi na garau garau ko gwaben zogale, rama da sauran su ,a biyo ni dakin girki In Sha Allah💃🏻

Read more
Edit recipe
See report
Share

Ingredients

  1. Karamin kwanu na kuli kuli
  2. 1/4Kofi na busasshen yaji (kina iya karawa in kina so)
  3. Citta kamar Rabin hannu
  4. 1 Tblsna kanunfari,
  5. 1 Tblsna masoro
  6. 1 Tblsna sukuni
  7. Kwarorin kamar 8 na gyadan/diyan Miya
  8. Kwara biyar na kimba
  9. Tspdaya na tumeric (basan sunan shi na hausa ba)
  10. Dandano dai dai da yadda kike so, ni nasa kwara hudu
  11. Bay leaves kadan (shima dai ban San shi da hausa ba)

Cooking Instructions

  1. 1

    Kuli na Yana da girma na Dan parpasa shi,kina Iya umfani da turmi.

  2. 2

    Nayi mixing duka da kayan Hadi na sanan na markade. Ina da blender Mai karfi Yana da yasu dayawa, yakan markade busasshen Kaya, Amma in blender din ki Bai da karfi Yana iya lalata Miki, so sai ki Kai wurin markade.

  3. 3

    Sai ki sa a container Mai murfi ki rufe ki Adana.

  4. 4

    Dadi har cikin kwanya😅. Yanzu haka na Dora wake na Zan Yi garau garau💃🏻💃🏻. Ina ma zan Samu rama a Legas ne😀 yau in Sha datu😀

Reactions

Edit recipe
See report
Share

Comments (10)

FolSt
FolSt @cook_29700985
Hi MJ's kitchen, Thanks for your recipe. Please can you translate it into English. Thank you

Written by

MJ's Kitchen
MJ's Kitchen @mjrena
on
Lagos
I love cooking and sharing my recipes.
Read more

Similar Recipes