Share

Ingredients

  1. shinkafa normal ta dafawa bata tuwo ba -kifi -tattasai -taruhu
  2. ganyen zogale -ganyen alayyahu -maggi -mai -Curry -gishiri

Cooking Instructions

  1. 1

    Idan shinfanki qalau yake bakya buqatan gyara zaa barza shi kar yayi laushi kamar dai niqan biski/burabusko wara-wara saiki juye a roba mai fadi ki wanke shi ki zuba a steamer ki dora wuta ki barshi ya turara sosai.

  2. 2

    Zaki dauko kayan miyan ki ki jajjaga taruhu da tattasai, albasan kuma ki yanka manya-manya haka koren tattasa ma ki yanka shi, saiki dauko kifin ki ko wane iri ne ki wanke shi kisa dandano da kayan qamshi ki tafasa shi da ruwa kadan yadda zai tsane jikin kifin.

    Zaki gyara ganyen zogalen ki ki wanke sosai ki gyara alayyahu ma ki wanke sosai ki yanka allayahun,

  3. 3

    Idan shinkafan ki yayi zaki sauqe ki hada shi ki juye duk kayan ki, maggi, gishiri, kifi, mai tattasai, taruhu, curry, koren tattasai, da albasan saiki mixing garin shinkafan sosai ko ina ya hade sannan saiki maida shi cikin steamer ki sake dora wa a wuta ki barshi har ya dahu zaki ji qamshi, Amma ana saka gyada in kinaso zaki iya sakawa, #AYYUSH

Edit recipe
See report
Share

Cooksnaps

Did you make this recipe? Share a picture of your creation!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Ayyush_hadejia
Ayyush_hadejia @cook_14256791
on
Jigawa State Nigeria

Comments

Similar Recipes