Sinasir with miyan taushe & Kunun aya

Asmau Maikaba
Asmau Maikaba @cook_16090052
Edit recipe
See report
Share
Share

Ingredients

Cooking Instructions

  1. 1

    Da farko zaki jika white rice dinki overnight,sai akai a niko,amma kada a cika ruwa a markaden.

  2. 2

    Ana kawo markaden na zuba yeast na rufe for 20 min,yana tashi saiki juya ki zuba sugar,baking powder sai salt kadan,saiki kuma juyawa ki barshi for 10min,

  3. 3

    Saiki dora kaskon ki akan wuta ki zuba kullin in a low heat ki rufe da murfi,in yayi saiki cire ki zuba wani

  4. 4

    MIYAN TAUSHE Kiwanke namanki ki dora a wuta da maggi da kayan qamshi, Albasa, inkin tabbatar yai laushi kisauke ki fere kabewa ki yanka, kiwanke kayan miyar kihada da kabewar ki dafasu insunyi laushi ki blending ko kidaka a turmi,saiki Dora mai a wuta ko fari ko ja ko mix saiki zuba kayan miyar ki akan man ki kawo dakakkiyar gyada inkinaso ki zuba kizuba namanki, kisa kayan qamshi seasoning intai kauri ki zuba ruwan sulalen inba,bu kisa ruwa iya yanda kikeson kaurin inta dahu kisaka ganye minti

  5. 5

    Aya
    Dabino
    Kwakwa
    Madarar gari
    Ginger
    Kananfari
    Vanilla ko coconut and banana
    YADDA AKE HADAWA
    Dafarko zaki samu aya mai kyau sai ki jikata tunda safe ko kuma a kwara mata ruwan
    Zafi abarta tayi 30min, sai a surfata a turmi.
    Idan an surfa sai a wanketa tas asa ginger da kananfari da dibino amma sai an cire kwallayon an wanke, da kwakwa itama sai an fere bakin bayan sai ayanka kanana sai akai a markada ko a markada a bulanda.

  6. 6

    Idan an markada sai a tace a saka madara,sugar da flavor a gauraya,sai a saka a fridge ko a zuba kankara

Edit recipe
See report
Share

Cooksnaps

Did you make this recipe? Share a picture of your creation!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Asmau Maikaba
Asmau Maikaba @cook_16090052
on

Comments

Similar Recipes