Moimoi with cabbage sauce

Mrs Mubarak
Mrs Mubarak @maanees_kitchen

#teamsokoto Nayi wannan girkin ne saboda mai gida yayi azumi. Nasan zaiji dadinshi lokacin buda baki kuma yayi farin ciki 💃🏼😋💃🏼

Moimoi with cabbage sauce

#teamsokoto Nayi wannan girkin ne saboda mai gida yayi azumi. Nasan zaiji dadinshi lokacin buda baki kuma yayi farin ciki 💃🏼😋💃🏼

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Wake
  2. Mai
  3. Sinadarin dan dano
  4. Ledar dauri
  5. Tattasai
  6. Tarugu
  7. Albasa
  8. Curry
  9. Kwai
  10. Cabbage

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko na surfa wake na wanke na tsince hancin wake na yanka kayan hadi na markada a bleder

  2. 2

    Bayan na markada na zube a mazubi nasa kayan hadi tare da mai na motsa

  3. 3

    Bayan na gama nasa a leda na daure nasa a tukunya dan ya dahu

  4. 4

    Sannan na fasa kwai na yanka albasa nasa magi na kada na soya nayi mishi gutu gutu saboda zaifi kyau

  5. 5

    Na zuba mai nasa albasa ya fara soyuwa nasa cabbage da tattasai tarugu da albasa na fara soya ya fara soyuwa nasa yaji da curry da gani

  6. 6

    Bayan kayan hadin sun hade na dauko soyayyen kwai nasa na kara motsawa saboda ya hade ko ina

  7. 7

    Bayan nan sai batun ci
    Na zuba a plate

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Mrs Mubarak
Mrs Mubarak @maanees_kitchen
rannar

Similar Recipes