Dambun nama

teezah's kitchen
teezah's kitchen @cook_14114675
Kano

Sallah tazo ana sarrafa nama kala kala, dambun nama yana ciki. #layya

Dambun nama

Sallah tazo ana sarrafa nama kala kala, dambun nama yana ciki. #layya

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

4hrs
5 yawan abinchi
  1. Tsokar nama kamar cinya
  2. Mixed Maggie (star mr chef, knorr, Ajino, onga)
  3. spices (cinnamon, cardamom, black pepper, cloves, corriander)
  4. Curry
  5. jajjagen attaruhu da albasa

Umarnin dafa abinci

4hrs
  1. 1

    Zaki sami nama tsoka zallah ki yayyanka ki zuba komai dana lissafa a sama Maggie spices da jajjage, kisa ruwa isashe

  2. 2

    Zaki barshi a wuta yayi ta dahuwa for 3-4 hours, wuta sosai, idan kina da pressure pot 1 hour ya dahu, zaki ga ya fashe kina diba

  3. 3

    Zaki daka shi a turmi sosai ya daku

  4. 4

    Zaki hada wuta ki dora abun suya ki zuba naman, kisa wutar yar dai dai ko Ina yana ci amma kar ki cika, ki fara jujjuya shi idan yayi fari sai ki zuba albasa, ki kara Maggie da mixed spice kadan da ginger, sai ki saka mai dan dai dai kici gaba da juyawa

  5. 5

    Kiyi ta juyawa har ya fara brown, sai ki zuba curry dinki.

  6. 6

    Zaki ci gaba da juyawa har sai kwanon ya daina kama naman kuma kin taba kinji ba danshi, sai ki kwashe, amma kiyi hankali kada yayi brown ya kone yayi daci

  7. 7

    Sai ki juye a tray ki warware wanda ya dunkule ki baza a tray yasha iska

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
teezah's kitchen
teezah's kitchen @cook_14114675
rannar
Kano
cooking is my hubby my favorite
Kara karantawa

sharhai (2)

Jamila Ibrahim Tunau
Jamila Ibrahim Tunau @Jamitunau
An zuba fasaha gurin nan😍
masha Allah😋

Similar Recipes