Dambun Namar Rago

RuQus
RuQus @cook_17712169
Kaduna

Dambun nama wani hanyar sarrafa nama ce ta yanda zaka samu naman a wani yanayi na daban amma ba tare da kayi kokarin chanza ma naman 'dan'dano ba ko 'kara wani abu a ciki dazai chanza masa siffa. Abunda yasa nake 'kaunar dambun nama kenan kuma wannan wani hanya ne mafi sauqi nayin Dambun nama ga kuma da'di da zaqi 😋 #Namansallah

Dambun Namar Rago

Masu dafa abinci 100+ sun ziyarci wannan girkin

Dambun nama wani hanyar sarrafa nama ce ta yanda zaka samu naman a wani yanayi na daban amma ba tare da kayi kokarin chanza ma naman 'dan'dano ba ko 'kara wani abu a ciki dazai chanza masa siffa. Abunda yasa nake 'kaunar dambun nama kenan kuma wannan wani hanya ne mafi sauqi nayin Dambun nama ga kuma da'di da zaqi 😋 #Namansallah

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Minti Arba'ina
  1. Naman Rago
  2. Garin Citta
  3. Garin Curry
  4. Kayan Kamshi
  5. Gishiri
  6. Sinadaran 'Dan'dano
  7. Albasa yankakke
  8. Jajjagen kayan miya ko yaji
  9. Man Gya'da

Umarnin dafa abinci

Minti Arba'ina
  1. 1

    Yanka wani sashi na naman rago mai tsoka azuba a tukunya

  2. 2

    Azuba ruwa madaidaici adaura kan wuta

  3. 3

    Zuba yankakken Albasa, Gishiri, Garin citta, Garin Curry, kayan Kamshi da a caku'da a rufe abarshi a wuta yayita dahuwa har sai naman yayi taushi.

  4. 4

    Bayan nama yayi taushi a kwashe a tsane a wani mazubi ko kwando.

  5. 5

    Samo Turmi da ta'barya a goge ciki a zuba kayan miya da Albasa a jajjaga sai a qara da tsokan naman a ciki a ha'da a jajjaga har sai yayi laushi sai a kwashe.

  6. 6

    Azuba sinadaran dandanon a ciki a caku'da a ajiye gefe

  7. 7

    Daura kaskon suya a wuta a zuba man gyada aqalla gwangwani 2

  8. 8

    Bayan yayi zafi azuba dakakken naman aciki a soya har sai ya warware ya soyu

  9. 9

    A tsane naman awani matsani a ajiye gefe harsai mangyadan ya tsane sai a zuba aci 😋

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
RuQus
RuQus @cook_17712169
rannar
Kaduna
The most interesting thing about life is Food! Foodie ❤️
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes