*My first recipe contest*Soyayyar shinkafa,lemun cucumba,salad

*My first recipe contest*Soyayyar shinkafa,lemun cucumba,salad
Steps
- 1
Za'a fara wanke shinkafa sai a zuba ruwa a tukunya a dora ta a wuta. Ka barta ta tafaso kamar saubiyu. Daga nan zaka sauke ka zuba cikin kwando mai hanyoyi sai ka zuba mata ruwa mai sanyi har sai zafin ya fita. Sai kabarta a kwandon ta tsane.
- 2
Zaka Dora tafashen nama ka saka kayan dandano da albasa sai ka rufe abarshi harya dafu. Idan ya dafu zaka cire daman sannan sauran ruwan nama za'a ajiye gefe. Daman shima za'a soya a ajiye.
- 3
Zaka dauko kayan lambun ka wanda zaka saka cikin shinkafa. Zaka yanka su da dan girma yanda zasu fito cikin shinkafa. Idan ka gama yankawa zaka saka ruwa a tukunya. idan ya tafaso zaka zuba kayan lambun ka da ka yanka sai ka zuba baking powder kaman cokali daya na shan shayi. Idan ya tafaso daya sai ka sauke tsane shi a kwando ka ajiye gefe. Amfanin yin haka shi zaisa idan ka zuba kayan lambun ka cikin shinkafa color din su bazai cenza ba zasu fito zar sha'awa.
- 4
Zaka nemo tukunya zaka zuba man gyada ciki. idan ya dau zafi zaka zuba yan karkiyar albasa ciki ka bata mintuna biyu. Saika dauko shinkafan ka da ka tafasa saika zuba ciki. Itama ka dan bata mintuna kana juyawa. idan ta dan fara soyuwa sai ka dauko ruwan tafasan nama ciki. Sai kara da ruwa idan na tafasan ba zai isa ba.sai ka zuba kayan dandano da su curry da sauran kayan kamshi saika rufe ka barshi
- 5
Idan ruwan girkin yaso ma tsotsewa shine zaka zuba su kayan lambun ka da ka tafasa da su anta koda.sai ka juya ya hade ko ina.saika sake rufewa ka barshi harya tsane. Idan ya tsane zaka kashe wuta saika sauke. shikenan an gama da shinkafa. Dan ba'a so su dafe ciki shiyasa ake bari sai ruwan girki ya kusa shanyewa
- 6
Dagana zaka dauko kayan lambun ka da zakayi salad dasu. Zaka saka abin gugan kubewa ka goge su cabeji da karas.sannan ka yanka lattas kananu. Saika wanke ka tsane su. Saika hada su guri daya. Ka zuba salad cream da mayonnaise ka yamotse. Shikenan ka gama dashi.
- 7
Shikuma lemun cocumba. Zaka wanke cocumba saika yanka ta cikin blender sai ka markada ta. Idan ta niku sai kama matse lemun tsami ciki dai dai yanda kakeso. sai ka tace dusan ka fidda ruwan. Daga nan zaka zuba sugar,flavor da food color sai ka juya ka saka cikin fridge yayi sanyi.
Similar Recipes
More Recipes
-

Ifeoma John
-

Bushra Mazhar
-

Bushra Mazhar
-

Black Pepper Velvet Cream Cheese Spread
Bianca Mwale
-

Hania Hameed
-

Sweet Cabe
-

Maggie Conlon
-

Bushra Mazhar
-

Traditional Thali with Bajri Bhakhri
Darshana Patel
-

Chili Cheese Dog Bubble Up Casserole
Christina
-

Mrs. Griffin
-

So Yummy
-

Meatloaf That’s Actually Delicious 🤤
Mrs. Griffin
-

Julie T.
-

Fatima Dewa
-

MangoIceCreamwithChocolateCakes
Khalida Arain
-

Vittlesbites
-

mum ashraf's kitchen
-

Mital Viramgama
-

Saryia Shariq
-

Ruchi Chopra
-

Shinkafa me curry da miyar kifi
HABIBA AHMAD RUFAI
-

Mom mufeedah
-

Akriti Sharma





Comments