Kunun Gyada na Shinkafa

Rahma kabir
Rahma kabir @rahmakabir
Kaduna

#1post1hope. Ina son kunun gyada musamman na sha da kosai, kunu ne daya samo asali daga Garin Maiduguri akwai dadi da gardi sosai.

Kunun Gyada na Shinkafa

#1post1hope. Ina son kunun gyada musamman na sha da kosai, kunu ne daya samo asali daga Garin Maiduguri akwai dadi da gardi sosai.

Edit recipe
See report
Share
Share

Ingredients

  1. Gyada 1/2 kwano
  2. Shinkafar tuwo, gwangwani daya da rabi
  3. Tsamiya
  4. Sugar
  5. Danyar citta
  6. Kanunfari
  7. Madara (optional)

Cooking Instructions

  1. 1

    Ki jika tsamiya a cup, Ki jika gyada tayi kamar awa daya, ki wanke ki murje bawon ya fita saiki sanya danyar citta da kanunfari ki kai nika. In an kawo ki tace da abin tace kamu ko rariya, ki cire dusar ki zubar, ruwan ki zuba a tukunya ki daura a wuta.

  2. 2

    Inya tausa ki wanke shinkafar ki zuba a cikin ruwar gyadar ki rufe kadan amma ba duka ba saboda kar yayi kumfa ya zube. Idan shinkafar ta dahu za kiga ruwar gyadar ya ragu yayi dan kauri saiki rage wutan, ki tace tsamiyar ki zuba a cikin kunun kina juyawa da ludayi nan take zaiyi kauri ya hade jiki, sai ki dan bari ya kara mintuna ki sauke ki sanya sugar, ki zuba a mazubi. In za'a sha a sanya madarar gari a juya akwai dadi, in kuma baki son madarar ki barshi.

  3. 3

    Note: idan kin cika ruwa a lokacin tace gyadar, kunun yazo ya miki ruwa, to zaki iya dama fulawa ko gasarar koko ki daure dashi. Zaki iya amfani da Lemun tsami a madadin tsamiya, dan tsamiya tana sanya kunun yadan yi hudu. Na sanya Gyada rabin kwano saboda muna da d'an yawa gidan mu, in ba kuda yawa zaki sanya dai-dai yanda zai muku, zaki iya kara shinkafar in kina so ta fito sosai, ni na sanya gwangwani daya da rabi dan bana so ta fito sosai.

Edit recipe
See report
Share

Cooksnaps

Did you make this recipe? Share a picture of your creation!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Rahma kabir
Rahma kabir @rahmakabir
on
Kaduna
I love cooking.
Read more

Comments

Similar Recipes