Jolof din shinkafa da wake da soyeyyen kifi

sunusi Zainab
sunusi Zainab @cook_17397928
Ni Yar Kaduna Ce

Nida iyalina munasan wannan girkin.

Jolof din shinkafa da wake da soyeyyen kifi

Masu dafa abinci 100+ sun ziyarci wannan girkin

Nida iyalina munasan wannan girkin.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

1 hour
  1. 3/cup shinkafa
  2. 1/2wake
  3. 1/2 cupmangyada
  4. Timatar
  5. Tarugu
  6. Tattasai
  7. 1/ albasa babba
  8. 1/2curry
  9. 5/6maggi
  10. 1/2spices
  11. Kifi

Umarnin dafa abinci

1 hour
  1. 1

    Da farko dai zaki fara jika wakenki a ruwa kafin ki fara komai Dan yayi saurin dahuwa ki aje agefe.

  2. 2

    Sai ki jajjaga kayan miya timatir tarugu tattasai da albasa, ki aje agefe sai ki yanka kifinki ki wankeshi ki tsaneshi kidan sa mai gishiri kadan.

  3. 3

    Sai kisa mai awuta iyayi zafi kidan samai yar albasa tasoyu sai kisa kifinki yasoyu inya soyu ki kwashe shi sai ki zuba kayan miyanki kita juyawa har sai ya soyu sai kisa curry da spices sai ki zuba ruwa dai dai yadda zai dafa miki abinci sai ki dako waken da kika jika sai kizuba sai ki rufe.

  4. 4

    Idan ya tafarfasa kin tabbatar da wakenki ya dahu sai kisa maggi da Dan gishiri kadan sai ki wanke shinkafarki ki zuba sai ki juya sosai Dan su hade da wakensai ki rufe zuwa 20minite.

  5. 5

    Idan kika bude kikaga ruwan ya fara ja baya sai ki yanka albasanki ki zuba sai ki dauko soyyan kifinki ki Dora akai sai ki rufe ki rage wuta zuwa 10 minite abinci ya dahu saici.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
sunusi Zainab
sunusi Zainab @cook_17397928
rannar
Ni Yar Kaduna Ce
INA maturar San girki kala kala
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes