Yadda ake hada awara(Tofu)

Khady Dharuna
Khady Dharuna @antynanah2022
Kano, Meduguri Road, Tarauni.

Memakon muyi ta siyan awara gwara mu hada da kanmu ko Dan kula da lfyr mu. Wanna. Shine karo.na 2 da nayu kuma tayi kyau sosaj.Tanada auki sosai.

Yadda ake hada awara(Tofu)

Masu dafa abinci 15 suna shirin yin wannan

Memakon muyi ta siyan awara gwara mu hada da kanmu ko Dan kula da lfyr mu. Wanna. Shine karo.na 2 da nayu kuma tayi kyau sosaj.Tanada auki sosai.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Waken awara Rabin kwano (soya beans)
  2. 5 tblsManja
  3. Ruwa
  4. Ruwan tsami/ ruwan gasara
  5. Abin tata

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    A gyara wake a cire dattin.

  2. 2

    A wanke shi a rege tsakuwar da kasar da ke cikinsa ya fita tass, sannan a kai a markado.

  3. 3

    Idan aka markado sai a zuba masa manja a juya. Ana saka manja ne sbd yana yin kumfa

  4. 4

    A juya sosai sai a zuba ruwa a tace a kula kar a cika ruwa sosai yanda dai zai fita.

  5. 5

    A fitar da dusar

  6. 6

    Sai a juye a cikin tukunya babba sosai a dora akan wuta a dunga kula a barshi ya tafasa.

  7. 7

    Yana tafasowa za aga kumfa Tayi sama

  8. 8

    Sannan a sami ruwan tsami ko ruwan gasara a zuba akai

  9. 9

    Idan an zuba ruwan tsami za a ga tana hade jikinta

  10. 10

    Sai a barta ta karasa hadewa sannan a juye a abun tata a matse.

  11. 11

    Sannan a kulle bakin abin a dora mata abu me nauyi ta tsane sosai

  12. 12

    Idan ta tsane sai a yayyanka.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Khady Dharuna
Khady Dharuna @antynanah2022
rannar
Kano, Meduguri Road, Tarauni.
cooking is my dream!!!
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes