Madarar waken soya.(soya milk)

mrs gentle
mrs gentle @MAS09

Nakasance mai son madarar wake soya ta kwalba, hakan ya bani kwarin gwuiwar koyon yinta a gida. Nida iyalina munyi na'am da wannan madarar saboda dadi da kuma amfaninta a fanin lafiya.#Lemu

Madarar waken soya.(soya milk)

Nakasance mai son madarar wake soya ta kwalba, hakan ya bani kwarin gwuiwar koyon yinta a gida. Nida iyalina munyi na'am da wannan madarar saboda dadi da kuma amfaninta a fanin lafiya.#Lemu

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Waken soya
  2. Danyar gyada
  3. Citta
  4. Kanunfari
  5. Madarar ruwa
  6. Suga
  7. Flavour na vanilla

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    A tsince waken a fitarda datti a cika shi a cikin ruwa.itama gyadar a stince ta a gyara sai a jika, bayan kamar awa 3 sai tsiyaye ruwan a wanke su duka.(ba sai an cire bawarsu ba) sai a saka citta da kanumfari akai nikka.

  2. 2

    Idan an niko sai a tace.kada a saki ruwa gurin taci.

  3. 3

    Sai a juye a tukunya a daura a wuta

  4. 4

    A barshi kan wuta yayita tafasa, idan yayi sai sauke a bari yasha iska sai a sake tacewa, sai a xuba sugar,madarar ruwa da flavour.

  5. 5

    A sha da dumi ko a saka a cikin freezer yayi sanyi.

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
mrs gentle
mrs gentle @MAS09
rannar

sharhai

Similar Recipes