Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. 2Flawa kofi
  2. chokaliBaking powder karamin
  3. chokaliGishiri rabin karamin
  4. 2Tarugu guda
  5. Albasa karama
  6. 1Dandano guda
  7. Mai babban chokali 2
  8. Kayan kanshi
  9. Ruwa dai dai bukata
  10. Mai na suya

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko ki zuba flawar ki a roba sai ki zuba gishiri dandano,kayan kanshi da baking powder ki juya.sannan ki jajjaga tarugu ki yanka albasa kanana ki zuba ki juya.

  2. 2

    Sai ki zuba mai ki juya sannan ki rika zuba ruwan kadan kadan kina kwabawa.kar yayi tauri sosai kuma kar yayi ruwa. Sai ki rufe ki bashi minti goma.

  3. 3

    Bayan minti goma sai ki rika gutsiran kadan ki fadada shi da rolling pin sai ki sa kofi ko cutter ki fitar da shape don ya baki round sai ki soya a mai.Amma kar ki cika wuta,idan yayi ja sai ki kwashe.Ana iya ci da sauce ko sauce din dankali.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
mhhadejia
mhhadejia @mhhadejia1975
rannar
Kaduna State, Nigeria

sharhai

Similar Recipes