Soyayyar shinkafa

Delu's Kitchen
Delu's Kitchen @delu2721
Sokoto State

Foodfoliochallenge soyayyar shinkafa girkine mai dadin gaskiya shinkafarki zatayi warara gakuma daukan ido ga dadi acikin baki

Soyayyar shinkafa

Foodfoliochallenge soyayyar shinkafa girkine mai dadin gaskiya shinkafarki zatayi warara gakuma daukan ido ga dadi acikin baki

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Shinkafa da kika dafa tayi rabin dahuwa kofi biyu
  2. 3Tarugu
  3. 1Tattasai
  4. Albasa babba guda
  5. 2 tbspCurry
  6. 1 tspMix spices
  7. 1/3 cupMangida
  8. Koda ko Anta
  9. Tafarnuwa3
  10. Danyar citta Rabin guda
  11. 4Maggi
  12. Gishiri kadan
  13. Karas 2 manya
  14. 1/2 cupDanyen wake

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki saka mai a tukunya wadda bata kamawa (non stick) sai kisa albasa

  2. 2

    Sai kisa tattasai,tarugu,da kika wanke kika jajjaga ko kika gurza,sai tafarnuwa da danyar citta da kika daka,sai ki juya ya hade

  3. 3

    Sai kisaka kayan kamshinki da curry da maggi ki juya,sai kisa Karas da kika wanke kinka kanana sai ki juya zuwa minti daya

  4. 4

    Sai kisa soyayyar koda dinki wadda kika wanke kinka yanka kanana sai gishiri kadan kika soyata,sai ki juya komai ya game

  5. 5

    Sai kisaka shinkafarki da danyen wake da kika tafasa kika tsane ruwan,sai kiyita juyawa akai akai har zuwa minti 4 ko biyar sai ki sauke...Abun lura:-saboda yawan juyawa da zakiyi shiyassa baa son wajen tafasa shinkafar ka bari ta nuna sosai saboda soyawa zaayi in ba hakaba zata chabe

  6. 6

    Sai kisamu roba karama ki shafeta da mangida sai ki zuba shinkafarki ki danna sai ki jita ga plate dinki,kici da hadin salat

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Delu's Kitchen
rannar
Sokoto State
My name is Aisha Delu Aliyu known as Delu's Kitchen ,I love cooking ,cooking is my fav....
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes