Farfesun kaza(soyayyiya da dafaffiya me kayan lambu)

Khady Dharuna
Khady Dharuna @antynanah2022
Kano, Meduguri Road, Tarauni.

Ina son farfesu sosai musamman me kayan lambun yanada dadi ga kara lfy. Yana dadi ma Idan aka samu bread me laushi a hada dashi. #parpesurecipecontest

Farfesun kaza(soyayyiya da dafaffiya me kayan lambu)

Masu dafa abinci 3 suna shirin yin wannan

Ina son farfesu sosai musamman me kayan lambun yanada dadi ga kara lfy. Yana dadi ma Idan aka samu bread me laushi a hada dashi. #parpesurecipecontest

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

awa daya
mutane da yawa
  1. 4Kazar gidan Gona manya guda
  2. Attaruhu
  3. Albasa
  4. Kayan dandano
  5. 1/2 cokaliDakakkiyar citta
  6. Curry babban cokali 3
  7. Spices babban cokali 2
  8. 1Yankakken lawashi Kofi
  9. Tafarnuwa(domin bukata)
  10. Karas Rabin kofi
  11. Koren wake Rabin kofi
  12. Mai
  13. 5Lemon tsami manya guda

Umarnin dafa abinci

awa daya
  1. 1

    A yayyanka kaza yankan daidai ba manya ba kuma ba kana na ba. Sannan a wanke da lemon tsami sosai a tabbar karnin ya fita a tsane da kwalanda sai a juye a tukunya.

  2. 2

    A yayyanka albasa a zuba akai, a raba karamin lemon tsami ma a saka akai sai a Dora akan wuta

  3. 3

    A zuba spices cokali daya akai

  4. 4

    A zuba curry cokali 2

  5. 5

    A zuba dakakkiyar citta cokali 1

  6. 6

    Sannan a zuba Maggie daidai dandano

  7. 7

    A jajjaga tafarnuwa a zuba akai Idan ana bukata, sannan a juya a rufe ya dahuwa sama sama, bayan ya dahuwa sai a tsane a kwalanda.

  8. 8

    A raba kazar gida biyu sannan a Dora mai a yayyanka albasa Idan yayi zafi sai a zuba Rabin kazar a ciki a soyata har sai ta zama ruwan Zuma sai a kwashe.

  9. 9

    Sannan a dauko ruwan tafashen naman a raba shi biyu, a dau rabin a zuba jajjagaggen attaruhu da albasa a ciki a saka curry Rabin cokali spices ma Rabin cokali, sannan a zuba mai Dan daidai a Dora akan wuta, Idan ya tafasa sai a kara Magi a zuba yankakkiyar albasa a barshi ya dahu sosai yayi kauri.

  10. 10

    Sai a dauko soyayyar kazar a zuba wannan hadin akai a jujjuya koina ya samu sai a juye a mazubi

  11. 11

    Daga nan a Dora tukunya akan Wuta a zuba ragowar ruwan Tafashen Idan baida yawa a Dan kara ruwa sai a zuba jajjagen attaruhu da albasa, yankakken karas da mulmulallen wake, a rufe ya dahu.

  12. 12

    Idan sun dahu sai a kara magi, a saka ragowar kori da spices a zuba mai daidai misali sannan a kawo kazar da ba a dafa ba a zuba a zuba yankakken lawashi, sannan a juya a rufe ta turaru
    za aga ta farfashe sannan a kwashe.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Khady Dharuna
Khady Dharuna @antynanah2022
rannar
Kano, Meduguri Road, Tarauni.
cooking is my dream!!!
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes