Shinkafa da miyar Dankali

Mama's Kitchen_n_More🍴
Mama's Kitchen_n_More🍴 @cook_3357
Kano

Shinkafa Abar alfarina nidai a rayuwata Ina son shinkafa shiyasa nakan canja launin yadda zanci ta😍😋

Shinkafa da miyar Dankali

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan

Shinkafa Abar alfarina nidai a rayuwata Ina son shinkafa shiyasa nakan canja launin yadda zanci ta😍😋

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Awa daya
  1. Shinkafa Kofi daya
  2. Attaruhu guda biyar manya
  3. Albasa guda biyu
  4. Tomato na laida guda biyu
  5. Maggi
  6. Gishiri
  7. Seasonings/spices
  8. Man Kuli cokalin miya biyu
  9. Dankali guda uku manya

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Dafarko Zaki wanke hannu domin tsafta sai Dura ruwa a tukunya Mai tsafta idan ya tafasa sai a wanke shinkafa a zuba a rufe a barshi domin dahuwa,idan ruwan ya tsotso tayi laushe sai a sauke,a zuba a plat

  2. 2

    A cire hancin attaruhu a gyara albasa a hada da tomato a wanke ayi grating ko blending

  3. 3

    Sai a daura tukunya a huta a zuba Mai a yanka albasa idan tayi brown sai a zuba kayan miyan nan da akayi grating/blending sucigaba da daguwa

  4. 4

    Sai a dauko dankali a feraye a wanke a yanka idan kayan miyan sun fara alamun nuna sun dahu sai a zuba dankalin asa seasonings/spices a rufe su cigaba da soyowa har sai Mai ya fito a Saman miyan shine ta soyo

  5. 5

    Aci Dadi lafiya 😋

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Mama's Kitchen_n_More🍴
rannar
Kano
cooking is my hobby
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes