Masa da miyan ganye

ummukulsum Ahmad
ummukulsum Ahmad @cook_20521409
Abuja

Girki ne mai dadi da armashi,yayi matukar dadi, ku gwadashi

Masa da miyan ganye

Girki ne mai dadi da armashi,yayi matukar dadi, ku gwadashi

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Shinkafar tuwo gongoni hudu
  2. Mangyeda
  3. Yeast
  4. Gishiri
  5. Sugar
  6. Baking powder
  7. Dafaffen shinkafar tuwo
  8. Albasa
  9. ganyeMiyan
  10. Allayaahu
  11. Ogu
  12. Manja
  13. Nama
  14. Kashi (biscuit bone)
  15. Maggi
  16. Spices
  17. Tomatoes
  18. Attarugu
  19. Albasa
  20. Gitta
  21. Tafarnuwa
  22. Crayfish
  23. Ganda
  24. Bushashen kifi

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki gyra shinkafar tuwonki, ki cikata, da dare,da safe zai ki kara wonketa, kisa a maxubi, kixuba yeast teaspoon biyu,ki yanka albasa, a ciki,ki juye dafaffen shikafar tuwonki, aciki kadan, sai ki saka baking power, half teaspoon, kikai markade, inan kawo miki markade sai ki xuba sugar babbn spoon daya, da gishiri kadan,ki gauraya sosai,sai ki rufe,kisashi guri mai dumi, for like 1hr,ki duba inya tashi, sai ki kara yanka albasa a ciki, sai ki kawo kaskon suya,kisa a wuta,inyayi zafi

  2. 2

    Sai ki dinga saka mai,kina zuba kullin kadan kadan, kina yi kina dubawa karya kone,kina Kara mai,kina juya dayan bangaren, inyayi brown sosai, sai ki cire,kar kisa wuta dayawa, saboda yayi kyu....

  3. 3

    Sai miya kuma, zaki fara soya manja naki, inya soyu sai ki jajjaga albasa da attarugu, kizuba,da nikakken tomato koh tin ton tomatoes naki, gisoyashi kadan, sai ki xuba maggi dasu spaices naki, da tafarnuwa da jitta, ki juyashi, ki tabata komai yaji daidai, sai ki yanka allayahu da ogu naki, ki ajiye, sai ki koma kixuba cray fish, bushashen kifi, da nama, da biscuit bone naki, ki gauraya shi, sai ki ruf,ya tafasa kadan

  4. 4

    Sai ki kawo ganyen ki wonke da gishiri, kixuba dukk, kibarshi for like 5 minutes, sai ki sauke, shikenan,sai kici da tea koh kunu.....nidai da tea naci🤗

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
ummukulsum Ahmad
ummukulsum Ahmad @cook_20521409
rannar
Abuja
innason dafa abinci kala kala
Kara karantawa

Similar Recipes