Girgijen madara na cakuleti

Afaafy's Kitchen
Afaafy's Kitchen @mohana10
Kano

Dazu da yamma nazo daura girkina na sati sati da nk sakawa sai na kula da cewa wasu daga cikin girke girkena da na fara wnn tafiya dasu ta cookpad basa cikin jerin abinciccikan da na daura,na nemesu sama ko qasa na rasa....hk ya sosa raina,saboda ina matuqar ji dasu(duk da mafi yawansu basu da wani qarko,sabida babu hoto daki daki da sauransu)amma ina alfahari dasu ko ba komai dole suna cikin tarihin farkon tafiyata izuwa cookpad💚ynx kuma tunda na rasa su ina tunanin sake qaiqirar wasu daga ciki irinsu da wani salon sai in dawo dasu👌ba zan iya barin kundina babu su ba💯🤦‍♀️.....a min jaje😚

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

minti goma
2 yawan abinchi
  1. Kofi daya na na whipped cream (mai sanyi)
  2. 1/4kofi na majinar bature(condensed milk)
  3. Cokalibiyu na nutella
  4. Dogayen sanda biyu na cakuleti
  5. Kwalliya
  6. Kofinwhipped cream
  7. Cokalibiyu na nutella

Umarnin dafa abinci

minti goma
  1. 1

    Da farko za a zuba whipped cream,majinar bature cikin abin markade(na gida👏🤧)

  2. 2

    Sai a kakkarya sandar cakuleti shi ma a zuba a kai,a zuba nutella a rufe da murfi a fara markadawa.

  3. 3

    Zai dauki dan lokaci kafin sandar cakuletin ya nuqu,saboda sanyin cream din yasa yayi qarfi(za a riqa ji ma kamar ana niqa dutse ne)saboda hka za a iya kashe abin niqar a barshi ya riqa hutawa yana qara shan iska har a gama

  4. 4

    Bayan yayi laushi sai a samu kofin da za a zuba a debo nutella da cokali abi gefe da gefenshi ta ciki a shasshafe(ba sai ko ina ya samu ba)sai a zuba girgijen madarar

  5. 5

    Sannan ayi amfani da jakar piping da nozzle a zuba wani cream din a ciki a bi saman kofin ayi kwalliyar da ake so.....za a iya qara kwalliyar da yaryada nutella da kuma yan kayan marmari ko ma mene dai🤧

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Afaafy's Kitchen
rannar
Kano

Similar Recipes