Apple crepes

Jantullu'sbakery
Jantullu'sbakery @jantulluhadiza84
Sokoto

Muna godiya da cookpad classes na ayzah

Apple crepes

Muna godiya da cookpad classes na ayzah

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Apple daya da rabi
  2. Sugar cokali shidda
  3. Butter cokali ukku
  4. Lemon tsami daya
  5. Flour kofi daya
  6. Gishiri ¼ cokalin shayi
  7. Madara(fresh) kofi daya da kwata
  8. Kwai biyu
  9. Whipped cream
  10. Vanilla flavour cokali daya

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki wanke apple biyu ki fere bayanshi, ki yanka kanana ki ajiye gefe

  2. 2

    Zaki dauko pan ki dora akan wutan (wuta kadan) ki zuba butter cokali daya, ki zuba apple da kika yanka ki saka sugar cokali 3 ki juya harna tsawon mintuna 4 daga nan ki matse lemin tsami ki ci gaba da juyawa harna tsawon mintuna goma zuwa sha biyu sannan ki saukar ki ajiye gefe

  3. 3

    Domin yin crepe zaki zuba flour wanda kika tankade kofi daya a bowl, ki saka sugar cokali ukku da gishiri kadan ki juya sosai, zaki hada madara kofi daya da cokali 4 zaki fasa kwai 2 acikin madara kofindaya da kwata zaki zuba butter cokali biyu wanda ya narke aciki ki saka vanilla flavour cokali daya ki juya hadin madarar sosai kafin ki juye hadin madarar acikin flour ki juya sosai, sannan kiyi sieving ki cire duk wani dunkolen flour dake ciki

  4. 4

    Zaki dauko pan me fadi, shi saka butter yayi melting kafin ki dauko wannan kullun na flour ki zuba ji juya pan sosai saboda kullun y baje yayi round, idan dayan gefen ya gasu sai ki juya dayan gefen shima ya gasu

  5. 5

    Zaa dauko faifen crepe din a saka hadin apple din aciki, a zuba cream sannan ayi folding ayi garnishing da apple ko duk fruits din da uwargida ke raayi.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Jantullu'sbakery
Jantullu'sbakery @jantulluhadiza84
rannar
Sokoto
I love cooking,i love been creative and I love sharing my recipies 💓❣️💃
Kara karantawa

Similar Recipes