Shinkafa da wake (garau garau)

Ceemy's Delicious
Ceemy's Delicious @ceemys_delicious
Zoo Road Kano Nigeria

Shinkafa da wake itama tana daya daga cikin abincin gargajiya na hausawa. Shinkafa da wake tana da dadi musammanma idan taji mai da yaji mai dadi.

Shinkafa da wake (garau garau)

Shinkafa da wake itama tana daya daga cikin abincin gargajiya na hausawa. Shinkafa da wake tana da dadi musammanma idan taji mai da yaji mai dadi.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Awa 1mintuna
mutum 2 yawan abinchi
  1. 1 1/2Shinkafa Kofi
  2. Wake kofi⅓
  3. Ruwa na dafawa
  4. Mai cokali babba 2½
  5. Yaji yadda kike so
  6. 1Maggi
  7. Salak da tumatir domin kwaliya

Umarnin dafa abinci

Awa 1mintuna
  1. 1

    Dafarko xaki samu tukunyarki mai kyau, sai ki xuba ruwa dai dai misali, sannan ki rufe ki dora akan wuta. Kafin ya tafasa sai ki dauko wakenki ki tsinceh mai kyau din.

  2. 2

    Sannan ki duba idan ruwan ya tafasa sai ki xuba waken da kika tsinceh, ki rufe ki bar shi har sai yayi alamun ya fara dahuwa, sai ki dauko shinkafarki ki wanke ki xuba aciki.

  3. 3

    Bayan kin xuba sai ki barta tayi minti 20, sai ki xuba ruwa ki tace acikin kwalenda, sannan ki kuma mayar da ita cinkin Tukunyar ki xuba ruwa dan kadan ki barta ta turara.

  4. 4

    Kafin ta turara sai ki dauko salak da tumatir da cocomba ki wanke su sannan ki yanka. Bayan kin gama Sai ki duba shinkafarki ki ga idan ta turara sai ki sauke ki xuba acikin filate ki xuba mai, maggi, yaji, da kuma kayan gayen(salak) Shikenan kin gama sai ci😋💯💯

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Ceemy's Delicious
Ceemy's Delicious @ceemys_delicious
rannar
Zoo Road Kano Nigeria
my name Sumayyah Tahir Ibrahim, I live at zoo raod ja'oji, cooking,reading and research are my hobbies.
Kara karantawa

Similar Recipes