Shinkafa da wake(garau-garau)

Firdausy Salees
Firdausy Salees @cook_12401542
Kano

#garaugaraucontest. shinkafa da wake abincin hausawane mae dadi da farin jini,gashi kowa nasonsa,abincine da baa kashe kudi da yawa gurin yinsa amma sae dadi,ni bana wuce tayin garau-garau koda na koshi😂😂

Shinkafa da wake(garau-garau)

#garaugaraucontest. shinkafa da wake abincin hausawane mae dadi da farin jini,gashi kowa nasonsa,abincine da baa kashe kudi da yawa gurin yinsa amma sae dadi,ni bana wuce tayin garau-garau koda na koshi😂😂

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Sa'a daya (1hou
Mutum 8 serving
  1. Shinkafa kofi biyu (2)
  2. Wake rabin kofi (1/2)
  3. Gishiri cokali biyu (2)
  4. Ajinomoto karamar leda daya(1)
  5. Kanwa kadan
  6. Maggi mae tauraro guda biyu (2)
  7. Ruwa mae tsafta (na dafawa)
  8. Man kuli gwangwani daya (1)
  9. Yaji
  10. Ganyen salad,tumatur da albasa
  11. Kaninfari kadan
  12. Kiyi ado da yankan lemon tsami

Umarnin dafa abinci

Sa'a daya (1hou
  1. 1

    Da farko zaki gyara wakenki ki tsince tasss saeki wanke,ki zuba ruwa a tukunya da dan yawa sannan ki zuba waken,kisa gishiri da ajinomoto

  2. 2

    Kisa kanwa da maggi guda daya,kanwa na taemakawa wake gurin dahuwa da wuri hkama ajinomoto ko albasa,saeki juya ki rufe y dahu na tsahon rabin saa

  3. 3

    Nan ga shinkafarmu kofi biyu saeki wanke ki zuba acikin waken da yayita dahuwa na rabin saa

  4. 4

    Idan shinkafar ta hadu saeki tace sannan ki kara maedawa tukunya y turarah na mintina kadan...

  5. 5

    Saeki zuba mae a kasko kisa albasa ki soya,ki yanka salad ki wanke da gishiri ko vinegar...

  6. 6

    Sae aci da soyayyan mankuli,yaji,maggi da ganyen salad😋😋😋

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Firdausy Salees
Firdausy Salees @cook_12401542
rannar
Kano

Similar Recipes