Shinkafa da wake (garau garau)

Fateen
Fateen @Fteenabkr277

Shinkafa da wake yana daya daga cikin abincin da nafiso a duk sanda zan dafa ina acikin farinciki musamman irin dahuwar da kakata takeyi#garaugaraucontest

Shinkafa da wake (garau garau)

Shinkafa da wake yana daya daga cikin abincin da nafiso a duk sanda zan dafa ina acikin farinciki musamman irin dahuwar da kakata takeyi#garaugaraucontest

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

1 awa
5 yawan abinchi
  1. Shinkafa Kofi uku
  2. Wake Kofi daya
  3. Kanwa kadan
  4. Gishiri ma kadan
  5. Sai suga shima kadan
  6. Sai salad
  7. Albasa Dan soya mangyada
  8. Mangyada ko manja
  9. Dakakken yaji

Umarnin dafa abinci

1 awa
  1. 1

    Da farko uwar gida ko amarya zaki tsince shinkafar ki idan ta hausace idan kuma ta bature ce shikenan,in kin tsince ki ajeye agefe

  2. 2

    Sai ki dauko wakenki shima ki tsince duk wani datti da kwarin wake shim ki ajeye agefe

  3. 3

    Sai ki kunna murhu ko gas duk Wanda Allah ya hore miki uwar gida,sai ki daura tukunyar ki mai dauke da ruwa aciki sai ki rufe idan ya tafasa sai ki zuba wakenki ki saka kanwarki da kishiri kadan sai ki saka siga sai Ki rufe Kamar minti 30

  4. 4

    Idan wakenki ya dahu sai ki dauko Ki daura tukunyar shinkafa, ki daura tukunyar ki mai dauke da ki daura kan gas ko murhu idan ruwan ya tafasa ki zuba shinkafarki sai ki zuba gishiri kadan da man gyada kadan Dan zai taimakawa shinkafarki tayi lafa lafa tayi kyau karki zuba ruwa dayawa awajen dahuwar shinkafar, shinkafarki tana dahuwa sai ki sauke.

  5. 5

    Ki daura kaskon suyan man gyada ko man ja, ki zuba manki a kasko tare da albasa ki soya karki bari yayi baki ita albasar

  6. 6

    Zai ki dauko salad da tumatir dinki ki wanke shi ki yanka irin yankan da kike so.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Fateen
Fateen @Fteenabkr277
rannar

sharhai

Jamila Ibrahim Tunau
Jamila Ibrahim Tunau @Jamitunau
@cook_14224006 Garau garau baya bata mun rai saboda qauna 😅😋

Similar Recipes