Shinkafa da wake(garaugarau)

@Rahma Barde
@Rahma Barde @cook_15125852
Katsina

Shinkafa da wake abinci ne mai dadin gaske mutane da yawa suna sha'awarsa bade kamar idan akace da mai da yaji ce to lallai duk inda aka ganshi zaku ga mutane na shaawaraa ku gwada wanan ku gani kuma zaku so shi

Shinkafa da wake(garaugarau)

Shinkafa da wake abinci ne mai dadin gaske mutane da yawa suna sha'awarsa bade kamar idan akace da mai da yaji ce to lallai duk inda aka ganshi zaku ga mutane na shaawaraa ku gwada wanan ku gani kuma zaku so shi

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Shinkafa kofi daya
  2. Wake rabin kofi
  3. Yaji(barkono) rabin kofi
  4. D'and'ano
  5. 2Tafarnuwa
  6. Citta1
  7. cokali Kanufari kwatan
  8. Mai na gyada koh manja cokali hudu
  9. Ganye latas kofi daya
  10. 2Tumatur
  11. 1Albasa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Za ki gyara waken ki sai ki daura ruwa a wuta ki barshi har ya fara tausa sai ki wanke waken ki zuba a cikin ruwan nan ki dauko albasa manya guda biyu ki gyara ta ki wanke ta kada ki yanka ta ki jefa ta guda gudanta sai ki rufe

  2. 2

    Bayan minti goma zuwa shabiyar sai ki duba kiga wanken ki ya dahu idan kin ci kinji ya fara dahuwa sai ki cire wanan albasar da kika zuba ki dauko shinkafar ki ki wanke ta ki zuba cikin waken da kike dafawa sai ki rufe

  3. 3

    Sai ki duba bayan minti goma haka zuwa shabiyar idan ta dahu sai ki kwashe ki tsane ta ga abun tace shinkafa

  4. 4

    Sai ki zuba mai a tukunya ki yanka albasa ki soya shi amma kada ki bari albarsar ta soye dan yafi dadi

  5. 5

    Sai ki dawo akan yajin ki (barkono) ki daka shi kisa masa d'and'ano da su tafarnuwa citta kanufari da sauran kayan kamshi da kike so

  6. 6

    Ki yanka ganyenki da su tumatur da albasa da koren tattasai shikenan wake da shinkafar ki ya kammala

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
@Rahma Barde
@Rahma Barde @cook_15125852
rannar
Katsina

sharhai

Similar Recipes