Sinasir ll

Samira Abubakar
Samira Abubakar @samrataadam
Sokoto State

@Best of 2020. Wannan sinasir ya matukar yin dadi sosai

Sinasir ll

@Best of 2020. Wannan sinasir ya matukar yin dadi sosai

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

2hr
10 yawan abinch
  1. 4 cupShinkafa tuwo
  2. 1 cupdafaffiyar shinkafa
  3. 1 tbspYeast
  4. 1 tspBaking powder
  5. 1/4 cupSugar
  6. 1 tspSalt
  7. 1medium Onion
  8. Oil for frying

Umarnin dafa abinci

2hr
  1. 1

    Zaki wanke shinkafarki, sannan saiki jikata ta kwana. Bayan shinkafar ta kwana acikin ruwa,saiki zubarda da ruwan. Zaki diba shinkafa saiki dafata,bayan ta huce saiki diba cup daya na dafaffiyar shinkafar saiki zubata cikin shinkafar da kika jika. Akai wurin markade sai amarkada

  2. 2

    Bayan anmarkada miki shinkafar kamar haka

  3. 3

    Zaki diba 1tsp na yeast,saiki zuba warm water kadan ki dama yeast din,saiki zuba cikin kullun

  4. 4

    Sannan saiki motsa. Zaki rufe saiki dauki bucket din kisashi acikin rana kibashi kamar awa daya ya tashi

  5. 5

    Bayan ya tashi,zakiga yayi bubble aciki,saiki zuba sugar da km gishiri

  6. 6

    Sai kuma ki zuba baking powder ki motsa da kyau kitabbata komai ya game. Zaki iya yanka albasa idan kina bukata

  7. 7

    Saiki samu non-stick frying pan dinki kisaka mai kadan,saikiyi amfani da ½ cup kirinka dibar kullun kizuba,kiyi amfani da murfi tukunya ki rufe. Ammafa ki rage wuta kada ya gone

  8. 8

    Gashinan yayi. Haka zaki ringayi harkigama sinasir din dika

  9. 9

    Gashinan yanda yayi,zaki iya samun guda 15pcs

  10. 10

    Zaki iya cinshi da kowace irin miya kike bukata

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Samira Abubakar
Samira Abubakar @samrataadam
rannar
Sokoto State

Similar Recipes