Wainar gero

Umma Sisinmama
Umma Sisinmama @cook_14224461
Kano

A gaskiya wainar nan tayi dadi sosai godiya ga chef salma ta saboda ita tayi na gani nima nayi kuma munji dadin ta sosai nida iyalaina

Wainar gero

A gaskiya wainar nan tayi dadi sosai godiya ga chef salma ta saboda ita tayi na gani nima nayi kuma munji dadin ta sosai nida iyalaina

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki surfa gero saiki wanke shi tatas saiki jika shi tsahon minti 30 zuwa awa 1 saiki bayar a niko miki ki saka yeast da karkashi da gishiri kadan ki jujjuya saiki rufe ki saka a guri mai dumi ya tashi.

  2. 2

    Inya tashi ki fito dashi daman kin jika kanwar ki saiki zuba ki jujjuya ki daura tandar waina in tayi zafi ki saka mai ki zuzzuba inta soyu ki juya inta karasa soyuwa ki kwashe haka zakiyi tayi harki gama.

  3. 3

    Saiki zuba maggi da gishiri a turmi ki daka ki saka yaji saiki juye kuli-kulin ki lillisa ki juye a mazubi.

  4. 4

    Ki yanka kabeji kanana ki wanke da gishiri ki wanke tumatur da albasa ki yayyanka saiki zuba wainar a faranti ki zuba kuli ki yaryad'a mai ki saka kabeji da tumatur da albasa aji dadi lafiya.

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Umma Sisinmama
Umma Sisinmama @cook_14224461
rannar
Kano
I was born in kano state
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes