Farantin dankali

Afaafy's Kitchen
Afaafy's Kitchen @mohana10
Kano

#IAMACTIVE #FPCDONE Wannan girkin na dafa shi ne wa kaina,a gurin chops by halymatu naga wani kwando da tayi na doya sai nayi niyyar gwadashi,ni kuma ya kasance bani da doya sai dankali....to dama an san dankali yana da ruwa ba kamar doya ba(kuma sai nayi kuskuren qara barinshi ya kwana cikin ruwa)don haka da nazo yi sai ya bani matsala kwando ba zai yiwu ba shi ne kawai na yanke yin wannan farantin😂(in ya san wata bai san wata ba)to ga sakamakon dai kuskurena a gabanku....mahaifiyata ta yaba min bayan ta ci....da fatan kuam zaku gwada.....a cigaba da dahuwa cikin farin ciki🙌

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

minti 40mintuna
mutane 3 yawan
  1. Dankalin turawa guda biyar(madaidaita)
  2. Fulawa kofi daya
  3. Corn fulawa rabin cokali daya
  4. Dambun nama rabin kofi
  5. Albasa
  6. Attaruhu
  7. Karas guda biyu
  8. Ja da koren tattasai
  9. Parsley
  10. Sinadarin dandano
  11. Curry
  12. Cumin
  13. Mayonnaise
  14. Sweet sauce

Umarnin dafa abinci

minti 40mintuna
  1. 1

    Da farko za a fere dankali ne a wankeshi a zuba a tukunya da dan ruwa da gishiri a tafasa shi.A wani kaskon a zuba mai(cokali biyu) sai a debo jajjagaggen attaruhu da albasa a zuba ciki a riqa soyawa (da wuta a can qasa)ana juyawa,a zuba karas

  2. 2

    A qara soyawa na sakwanni talatin,sai a zuba curry da sinadarin dandano,a juya sai a zuba dambu a kai a cakude,sai a zuba kore da jan tattasai

  3. 3

    A zuba ganyen parsley sai a kashe wuta....sai a koma kan dankali. A qaramin kwano a zuba corn flour da damashi da ruwa kadan sai a zuba garin cumin da curry,a dauko dafaffen dankali a zubashi cikin kwano a faffasashi sosai,sai a juye corn flour a kai

  4. 4

    A zuba fulawa da dan sinadarin dandano a cakudeshi,a bade hannu da fulawa a riqa diba da kadan ana ta6eshi da tafi yayi fadi sai a soyasu cikin mai,in sun soyu za a iya amfani da tissue ta kitchen a tsane man jiki,sai a riqa diban hadin dambunnan ana zubawa a tsakiyar farantin a barbada mayo da sweet sauce da dan parsley.....😋

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Afaafy's Kitchen
rannar
Kano

Similar Recipes