Aloo puri da miyar yelo kori

Wannan abincin yan Indian ne kuma nasamo recipe din a wurin rishab kitchen wanda tayi a akushi da rufi satin da yawuce. Munji dadinshi sosai nida yarana mungode
Aloo puri da miyar yelo kori
Wannan abincin yan Indian ne kuma nasamo recipe din a wurin rishab kitchen wanda tayi a akushi da rufi satin da yawuce. Munji dadinshi sosai nida yarana mungode
Umarnin dafa abinci
- 1
Hadin dough. Zaki fere dankali kiwanke kizuba atukunya kisa ruwa kidaura a wuta kidafa. Bayan yanuna sai kisauke ki ajiye tahuce sannan ki tankade flour kizuba a bowl kisa ridi kizuba semolina da kurkur ki jujjuya sai kizuba mai ki mursikata sosai sannan kidau abun goge kubewa ki dau dankalin ki goge acikin hadin flour din kijujjuya sai kisa ruwa kadan kadan har kikwabashi sosai sai kirufe ki ajiye agefe zuwa minti goma ko sha biyar
- 2
Baya wadannan mintunan sai kidauko kisake kwabawa sannan kirabata kashi 15 sai ki dau daya kibarbada flour wurin da zaki murza sannan ki murzata tadanyi fadi kuma tafi round mai kyau. Haka zaki tayi daya bayan daya har kigama duka 15 din
- 3
Bayan kingama sai kidaura pan a wuta kisa mai idan yayi zafi sai kirage wutan sannan kidau daya kisa acikin mai din sannan kidauko babban chokali kina diban mai din kina zubawa akai zakiga yana kumbura yana tashi toh kici gaba har yaga tashi sosai sannan ki cire kisake saka wani haka zakiyi tayi har kigama soyawa duka. Sannan kisa a towel kirufe
- 4
HADIN MIYA. Zaki fere dankali guda bakwai duka kiwanke kidaura a wuta kidafa bayan yanuna sai kisauke kitsiyaye ruwan sannan kibari yahuce sai kidau whisker ki dagargazashi sannan ki ajiye agefe
- 5
Sai ki yanyanka su karas dinki da koren tattase tareda koren wake suma ki ajiye agefe sai kidaura tukunya a wuta kisa mai kadan sannan kizuba karas da koren wake kijujjuya na minti biyu zuwa uku
- 6
Sannan ki jajjaga attarugu kizuba aciki sai kizuba nikakken nama kijujjuya sannan kizuba ruwa dan dai dai sai kisa sinadaran dandano da curry da thyme tareda kurkur ki jujjuya sannan kizuba dankalin da kika dagargaza aciki sai kizuba koren tattase kidan juyawa sannan kirage wutan kibarshi yadahu sai kisauke shikenan angama
Similar Recipes
More Recipes









sharhai