Dubulan a sauqaqe

Afaafy's Kitchen
Afaafy's Kitchen @mohana10
Kano

#DUBLAN 🤣ina cikin duba saqonni ta whatsapp naga Aunty jamila cookpad ta turo hoto na dan bayani game da gasar😶ban iya dublan ba gsky,wasu a cikin mahadar ma naji suna basu iya ba nn take ta turo mana da yadda ake yi,to wnd ta turo na dudduba💋kuma alhmdllh na sami abinda nk so

Dubulan a sauqaqe

#DUBLAN 🤣ina cikin duba saqonni ta whatsapp naga Aunty jamila cookpad ta turo hoto na dan bayani game da gasar😶ban iya dublan ba gsky,wasu a cikin mahadar ma naji suna basu iya ba nn take ta turo mana da yadda ake yi,to wnd ta turo na dudduba💋kuma alhmdllh na sami abinda nk so

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Fulawa kofi daya
  2. Sugar babban cokali daya
  3. Mai cokali uku
  4. Lemon tsami
  5. Sugar rabin kofi
  6. Madara cokali uku
  7. Ruwa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ki tankade fulawarki cikin kwano ki saka madara da sugar ki juya

  2. 2

    Ki saka mai ki cakudeshi,snn ki zuba ruwa yadda zai isa miki kwabin yy dan qarfi

  3. 3

    Ki ajiyeshi kamar minti biyar ya dan saki jikinshi sai ki dauko ki riqa gutsuwa kina murzawa,ki fidda mishi fasalin da'ira snn ki rabashi gida biyu ki dauku qarshenshi ki dan shafa damammiyar fulawa don ya hanashi rabewa in ya shiga mai,snn zaki iya yin wani fasalin mai qayatarwa

  4. 4

    Ki daura mai a kan wuta in yayi zafi ba sosai ba ki soyashi

  5. 5

    A wata tukunyar daban ki zuba ruwa daidai misali sannan ki zuba sugar rabin kofi ciki ki daura kan wuta ki barshi yayita dahuwa sai ki matsa ruwan lemon tsami,iya fara kauri sai a juye a wani kwanon,in ya huce a ciki za a tsoma dublan din❤daya bayan daya har a kammala,za a iya barbada habba akai ko kanto😋

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Afaafy's Kitchen
rannar
Kano

sharhai (4)

Similar Recipes