Wainar shinkafa

hadiza said lawan
hadiza said lawan @cook_14446590
Kano Nigeria

wannan waina akwaita da laushi ga dadi koba miya zakicita da kuli ko sugar.

Kara karantawa
Gyara girkin
See report
Tura

Kayan aiki

awa biyu
mutum 10 yawan
  1. 8farar shinkafa kofi
  2. yeast chokali 2
  3. baking powder chokali 1
  4. kanwa ungurnu chokali 3
  5. 1sugar kofi
  6. 2mai kofi

Umarnin dafa abinci

awa biyu
  1. 1

    Dafarko na jika shinkafar sannan na wanke na nika saina barta bansa mata komai ba tayi kamar awa daya ahaka saida nazo kwanciya sannan na dama yeast da ruwan zafi saina hada kullin sannan na rufeshi nasa awuri mai dumi saida safe sannan na bude naga yatashi.

  2. 2

    Saina dauko nazuba masa baking powder,kanwa,da sugar nahada sannan na dora kaskona awuta nafara suya.

  3. 3

    Amfanin sa kanwa ungurnu acikin waina shine zatayi laushi sosai zakiga tayi kamar sosan katifa.

Yanayi

Gyara girkin
See report
Tura

sharhai (5)

Ameerah
Ameerah @meerah
Sai anjika kanwar KO ahaka fa asakata

Wanda aka rubuta daga

hadiza said lawan
hadiza said lawan @cook_14446590
rannar
Kano Nigeria
I'm Hadiza aged of 38 living within Kano municipal and I'm married. cooking is my fashion I really loved it more especially our traditional dishes
Kara karantawa

Similar Recipes