Butter cookies (yanayin narkewa😫♥️)

Wannan shi ma daya daga cikin girkunan maryama's kitchen ne da na dade da adana shi ina son gwadawa,duk da da nazo yin nawa na danyi sauye sauye da ya qara armasar da girkin🤩za a iya cin wnn abu da safe a hada da zazzafan coffee ko kuma duk sanda aka so tare da sassanyan moctail😉kamar yadda nima nayi
Butter cookies (yanayin narkewa😫♥️)
Wannan shi ma daya daga cikin girkunan maryama's kitchen ne da na dade da adana shi ina son gwadawa,duk da da nazo yin nawa na danyi sauye sauye da ya qara armasar da girkin🤩za a iya cin wnn abu da safe a hada da zazzafan coffee ko kuma duk sanda aka so tare da sassanyan moctail😉kamar yadda nima nayi
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko za a tatse leda daya ta simas(ko wata butter din,yawanci a 250g suke zuwa),sai a zuba icing sugar ayi amfani da mixer ko whisker a bugashi sosai har sai ya canza kala sannan ya hade jikinshi,sai a zuba majinar bature da qwai da zest a qara bugawa da kyau
- 2
A zuba garin girfa da dan ruwa cokali daya a qara cakudeshi,sai a tankade fulawa da corn flour lokaci daya a cikin kwanon,a hankali in aka tankade rabi aka cakude sai a zuba sauran daga baya a qarasa cakudeshi
- 3
Ba zai yi qarfi sosai ba,sai a samu piping bag ki bude bakinshi ki zura nozzle din ki daidaitashi da kyau sai ki samu kofi mai dan tsaya mara hannu ki bude bakinshi ki zura a cikin kifin,sai ki yi amfani da spatula ki riqa debo hadinki kina maidashi cikin piping bag dinki
- 4
Ki kunna abin gashinki(pre heating) sai ki samu farantin gashinki ki shimfideshi da takarda,sannan ki zo ki zana hadin cookies din a kan takardar kamar yadda yk a hoto,za kuma ki iya yin wani fasalin(da wannan irin hadin nawa,1M nozzle da makamancinshi ba zai miki ba saboda zest din da aka saka zai toshe hanya yasa ya riqa guggutsurewa)
- 5
Ki saka shi a abin gashi(za a iya na gargajiya,nima na fara aka dauke wuta da haka na qarasa)na tsawon minti 10 wutar sama da qasa(150 farenheit)har sai ya fara kalar dan duhu kadan🙌shi knn....
Cooksnaps
Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!
Similar Recipes
-
-
Dalgona cookies
Wannan biskit na yishi ranar farko da aka saka dokar hana fita a kano.Da farko nayi niyyar yin dalgona coffee ne wanda ake yayi a daidai lkcn,to gsky lokacin zuciyata bata kwanta da yinshi ba saboda ina tunanin zai yi daci,har na fara sai kuma na canza ra'ayina zuwa biskit saboda dama nayi kewarshi kwana biyu,nayi amfani da nescafe din da na buga ne da sauran butter cream da nayi amfani dashi kwana hudu kafin yin biskit din #FPPC Afaafy's Kitchen -
Lemon moctail na shudin (blue)curacao 😫💃
Wannan lemo na musamman ne da labarin qayatarwarshi ya samo asali daga wjn yar uwa ta musamman....Maryama's kitchen ♥️ Afaafy's Kitchen -
Butter chicken
Wannan girki ya samo asali ne daga arewacin qasar hindu tun wajejen shekarun 1950s. Manyan kayan hadinshi shi ne kaza,butter da tumatur, sauran duk qari ne dan fito da dandano na musamman. Na yi wannan girki ne domin kaina. Na tashi tun ina yarinya dalilin kallon fina-finansu na fara sha'awar al'adunsu, yarukansu da abincinsu, wannan yana daya daga cikin abincinsu da nake matuqar so. Afaafy's Kitchen -
-
Pancake(ba qwai ba butter)😅
#kano Na rasa sunan da zan bashi😶wainar fulawa mai sugar🤔....👌a sauqaqe ba tada jijiyar wuya za kiyi abinki🤣kmr wainar fulawa Afaafy's Kitchen -
-
Cookies
#OMN wannan cookie din na yi sa ne saboda na dade Ina ajiyan wani cornflour sai yanzu na samu damar an fani dashi sassy retreats -
Gasasshen nannadadden burodi mai kifi
Wannan abinci na yishi ne don siyarwa....nayi amfani da kifin gwangwani amma za a iya yinshi da kifi sukumbiya,nima dashi na saba yi yau na rasashi a inda nake shi yasa....ga yadda nayi nan a qasa ko kuma zaku amfana dashi.Ayi dahuwa cikin farinciki😊❤ Afaafy's Kitchen -
Chocolate sauce ll
Za a iya amfani dashi wajen kwalliya wa cake ko dangwalawa da kayan maqulashe Afaafy's Kitchen -
Gasasshen naman rago(tsire)
Tsire daya daga cikin abincin siyarwa na hanya ne da ahalina suke matuqar qauna(a taqaice dai duk wani nama😂)to an zo da nama ne da yawa da za ayi amfani ni da yar uwata a dakin girki tace gsky ya kamata ayi gashi,ni kuma nace biryani za ayi ta dage qarshe na sakar mata,ga sakamakon hkn a gabanku😁❤ Afaafy's Kitchen -
Girgijen madara na cakuleti
Dazu da yamma nazo daura girkina na sati sati da nk sakawa sai na kula da cewa wasu daga cikin girke girkena da na fara wnn tafiya dasu ta cookpad basa cikin jerin abinciccikan da na daura,na nemesu sama ko qasa na rasa....hk ya sosa raina,saboda ina matuqar ji dasu(duk da mafi yawansu basu da wani qarko,sabida babu hoto daki daki da sauransu)amma ina alfahari dasu ko ba komai dole suna cikin tarihin farkon tafiyata izuwa cookpad💚ynx kuma tunda na rasa su ina tunanin sake qaiqirar wasu daga ciki irinsu da wani salon sai in dawo dasu👌ba zan iya barin kundina babu su ba💯🤦♀️.....a min jaje😚 Afaafy's Kitchen -
Cookies
Inason cookies sosai sbd natashi naga mama nayinshi sosai,har na koya amma bantaba kawowa araina ba za 'ai mai wani ado kuma yayi kyau da dadi saida naga jahun tayi ,thanks jahun for the recipe. Maryamyusuf -
Zobo
Abin Sha na zobo ana yinshi ne tin iyaye da kakanni a arewacin nijeriya zobo Yana daga cikin abin Sha na hausawa a kasar hausa ana yawan yinsa sosai saboda yana da amfani ana samun zobo a jikin bishiyar yakuwa zobo Yana da amfani a jiki sosai Yana warkar da cutar hawan jini,Yana Kara jini a jiki,Yana taimaka wa wajen markada abinci da wuri aciki Kuma yana da Dadi sosai masana ilimin kimiyya sun gano cewa zobo Yana rage kiba,Yana maganin ciwon hanta, yana Kare jikin Dan Adam daga kamuwa da ciwon cancer(ciwon daji),Yana kariya daga kamuwa da kwayoyin cuta wannan zobon nayi amfani da Kayan ita tuwa masu qara lafiya a jiki kamar kokomba tana Kara karfin ido,lemon Zaki Yana qara sinadari mae gina jiki,na'a na'a da citta suna maganin mura gaba daya dae wannan zobon yana qara lafiya Kuma gashi akwai Dadi sosai idan kuka gwada zakuji dadinshi #zobocontest Fatima Bint Galadima -
-
Nadadden biredi
*Biredi yakasance abinci ne Wanda mafi akasarin mutane sunacin shi a kamar abincin Karin kumallonsu, an kasance ana sarrafa biredi ta hanyoyi da yawa shiyasa nace nima bari na koyarwa yan uwa wannan hanyar dana iya don karuwarmu baki daya, kuma danayi wannan resipi din naji dadinshi yan gidanmu ma sunji dadinshi ba'a magana yan uwa Ku gwada kuma Ku kwashi wannan dadin sai an gwada akan San na kwarai😍😍😍 #Bakeabread Husnerh Abubakar -
Chocolate da red velvet cake
#nazabiinyigirkiCake nau'i ne na kayan zaqi da ake cewa dessert da turanci. Ana cinshi bayan an gama cin abinci mai gishiri da a samu daidaiton dandano a harshe kuma suna da dadi sosai,sannan ana yinsu dandano daban daban. Na yi wannan cake din ne wa kaina da sauran 'yan gdanmu, amma mu ma ba qa'ida muke bi ba😂mun ji dadinshi sosai.Bayan an gama gasa cake din kamar yadda na yi bayani a qasa kar a yi garajen cireshi daga gwangwani a take, a barshi ya gama hucewa gaba daya dan gujewa fashewa. Afaafy's Kitchen -
Cinnamon alewar madara
#ALAWA.Ina matukar son cinnamon,shiyasa nake yawan jarraba shi a girke girke da dama. Jantullu'sbakery -
Red velvet cake (30 pieces)
Musamman domin 'yan kasuwa. A wancan satin na kawo mana bayani game da plain vanilla cake. A yau kuma zan kawo mana yadda ake yin red velvet cake, da kuma whipping cream frosting, dalla dalla yanda za a fahimta. Idan an bi exactly measurement da zan kawo in shaa Allahu za a samu 30-32 pieces na cake. Kuma cikakku babu ha'inci. Ku shigo daga ciki a yi tare da ku. #team6cake Princess Amrah -
Butter cookies
Wannan cookies yana da dadi matuqa ,baqi na sunji dadin shi sosaiFatima Ibrahim (Albint, s cuisine)
-
Cookies
Godiya me yawa gareki sadiya jahun , ta dalilinki na koya cookies kala kala Allah ya saka miki da alkhairi bana cikakken Sati banyi shi agidana ba kowa yana jindadinshi. Afrah's kitchen -
Dan waken gargajiya
#dan-wakecontest,ina son dan wake,musamman Wanda akayi shi a gàrgajiyance,domin ingañcinsa a jikin mu da lafiyàr mu. Shiyasa nima na hada nawa na gargajiya. Gà dadi ga dàndano. Salwise's Kitchen -
Donut
Ina son donut gaskia gashi yayi dadi sosai musan man idan aka hada shi da wani abu mai sanyi kamar zobo da sauran su @Rahma Barde -
Shawarma
#shawarma.Inason shawarma sosai ni da iyalina.Nakan masu bazata da wannan a duk lokacin da nakeson sasu nishadi da farinciki.Shawarma abinci ne sosai da nakeso domin yana dauke da sinadarai na kayan ganye wanda ke gyara fata tare da bamu kariya daga cututtuka da izinin Allah,cucumber ta na narkar da kitsen da ke jikin dan adamg,karas na bada kariya da cutar daji(ulcer),yana kuma taimakawa gurin rage ciwon zuciya da mutuwar jiki.Kabeji yana rage kumburi,kyaikayi da kuma hawan jini a kuma sinadarin protein wato nama a ciki.Nakan ci lokacin da bana bukatar wani abu mai nauyi a ciki. fauxer -
Vanilla ice cream
Idan kika gwada wannan ice cream din kin daina sayen na waje saidai kiyi maku keda iyalinki Kisha dadinku. Meenat Kitchen -
Biskit mai kostad(custard)
Na kasance ina yawan ganin hanyoyin yin biskit a gurin jahun delicacies,har ya kasance da zarar naga an turo girkin biskit to nasan itace🙄amma fa banda yanzu domin kuwa bata ajiye baiwar a tare da ita kadai ba,ta koya mana kuma muna qoqarin gwadawa🤗mun gode Aunty Sadiya. Afaafy's Kitchen -
Soyayyar doya me curry da miyar kwai
Wannan girki na da dadi acishi da safe tare da tea. Afrah's kitchen -
Kwalliyar donut(strawberry flavor)
Abu ne me matukar daukar hankali da kyau,bugu da kari,ga uwa uba dadi Fulanys_kitchen -
Yoghurt
Zaki iya hada yoghurt dinki a gida a saukake,gashi kinsan duk abin da kika hada da shi, ba sayen na waje ba Wanda Baki da tabbacin abubuwan da aka hada shi da shi. mhhadejia -
Gasasshiyar alala
Wannan alalar nayi ta ne a gurguje saboda an wayi gari gdanmu a cike yan uwa na nesa sun zo da safe kuma aka tashi da shirin yin alalar....naga kmr zai dau tsahon lkc saboda abin da yawa shi yasa na dibi yanki daga cikin markaden na shiga na rage hanya....gsky ni naga saurinshi bashi da daukar lkc Afaafy's Kitchen
More Recipes
sharhai