Kayan aiki

  1. Tamba mudu daya ko rabin mudu
  2. Dankalin hausa. Babba guda daya
  3. sugar
  4. citta
  5. kanumfari

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki wanke tamba, ki rege, ki jikata takwana,washe gari sai ki saka citta da dankalin hausa da kanumfari, saiki kai nika a nikamaki shi yayi laushi kamar dai na kamu

  2. 2

    Ki daura babban tukunya mai zurfi awuta,kizuba zuwa ya kai tsakiyar tukunyar haka.

  3. 3

    Sannan ki raba kullun gida 3 kidau gida 2 sai ki dama da ruwan sanyi, sannan kiduba tukunyar inta tafasa sai
    Kizuba kullun da kika dama cikin ruwan tafashen. kidama. zai dai zamana kamar dai talge kikayi

  4. 4

    Zakiyi ta juyawa sai ya nuna yayi kauri. Ba kuma kaurin tuwo ba😁kauri dai irin na talgen tuwo

  5. 5

    Saiki sauke. Kibari ya huce yanda zaki iya tsaka yatsarki ta tsaya ciki ba tareda ya konaki ba

  6. 6

    Sai ki dama kullunki da ta rage kizubata kan talgen kijuya ya hade sosai. Sai ki rufi kibarta indai tayi tofa dakanta zata tsinke. Inkuma takiyi to hakan zaki ganta kamar dai talgen bata tsinke ba

  7. 7

    Sai ki samo tata ki tace, kizuba sugar kisaka a fridge yayi sanyi

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Aisha Ardo
Aisha Ardo @cook_26614272
rannar
Abuja Nigeria

sharhai

Similar Recipes