Gashasshen sandwich na musamman

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan
Askab Kitchen
Askab Kitchen @askab24617

Wannan girkin yana da dadi a kuma saukin yi musamman da safe yayin Karyawa ko kuma ayiwa yara sutafi makaranta dashi.

Kara karantawa
Gyara girkin
See report
Tura

Kayan aiki

minti talatin
mutane hudu
  1. Buredi Mai yanka yanka
  2. Bota
  3. gwangwaniKifin
  4. Jajjagagen attaruhu, albasa,tafarnuwa da danyar citta
  5. Kayan dandano da kayan kamshi
  6. Albasa babba guda daya
  7. Kabeji karami
  8. Mai cokali biyu

Umarnin dafa abinci

minti talatin
  1. 1

    Asamu biredi Mai yanka yanka a shafeshi da bota a ajiye a gefe.

  2. 2

    Za'a zuba mai a cikin karamin kaskon yin miya sai a zuba yankakkiyar albasa a dan soya na minti biyu, sai a zuba jajjagagen su attaruhu dinnan acigaba da soyawa. Azuba kayan kamshi da kayan dandano, sai a zuba yankakken kabeji. Idan aka tabbatar duk sun soyu sai a dauki kifin gwangwani a tsiyaye man cikinsa sai a faffasashi azuba akai a cigabada juyawa har komai ya hade jikinsa.

  3. 3

    Akunna na'urar gasa buredi, sai a dauko wannan buredi mai yankayanka wanda aka shafa bota a jiki sai a zuba wannan hadin su kifin nan ajikin bari daya na buredin a tabbatar ko ina ya samu sai dauko wani buredin a rufe dashi.

  4. 4

    Sai a dinga Jera wannan buredin acikin na'urar gashin a rufeta. Idan ya gasu Za'aji rana kamshi. Sai a bude a cire a rabashi biyu.

Yanayi

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan

sharhai

Wanda aka rubuta daga

Askab Kitchen
Askab Kitchen @askab24617
rannar

Similar Recipes

More Recommended Recipes