Biredi mai yanka yanka dauke da nama

Fateen
Fateen @Fteenabkr277

Wato wannan girkin mai gidana yayi santinsa sosai yayi dadi ba kadan ba wollah ga wani kamshi da yake tashi hmmm

Biredi mai yanka yanka dauke da nama

Masu dafa abinci 5 suna shirin yin wannan

Wato wannan girkin mai gidana yayi santinsa sosai yayi dadi ba kadan ba wollah ga wani kamshi da yake tashi hmmm

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

50mintuna
3 yawan abinchi
  1. Beredi mai yanka yanka guda 6
  2. Nama
  3. Kayan kamshi
  4. Kayan dandano
  5. Kwai guda daya
  6. Burbushin buredi
  7. Kantu
  8. Albasa
  9. Attariku

Umarnin dafa abinci

50mintuna
  1. 1

    Da farko zaki wanke,yanka namanki yanka kana kana sai ki soya shi tare da wannan albasar,kisa tafarnuwa, attarigu da duk dai wani kayan kamshi da kike bukata karki manta da magi

  2. 2

    Sai ki dauko abin katakon murza fulawa.ki cire gefen biredin wato wannan wajen kalar kasa

  3. 3

    Sai ki murza su duk suyi lafe lafe

  4. 4

    Sai dauko namanki ki zuba akan biredin sai ki shafe gefe gefen biredin da kwai, sai ki Dora wani murzazzen biredi ki kora akanshi wato ki rufe shi.

  5. 5

    Sai ki Dan shafa kwai a saman shi ki barbada burbushin buredinki tare da kantunki

  6. 6

    Haka zaki tayi har ki gama,sai ki gasa acikin abin gashi.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Fateen
Fateen @Fteenabkr277
rannar

sharhai

Similar Recipes