Fish roll

TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA) @cook_15480513
Port Harcourt

Yanada saukin yi kuma yanada dadi sosai iyalina sunji dadinsa sosai. Zaka iyayinsa dasafe don yara sutafi makaranta dashi kokuma kiyiwa baki #GirkiDayaBishiyaDaya

Fish roll

Masu dafa abinci 5 suna shirin yin wannan

Yanada saukin yi kuma yanada dadi sosai iyalina sunji dadinsa sosai. Zaka iyayinsa dasafe don yara sutafi makaranta dashi kokuma kiyiwa baki #GirkiDayaBishiyaDaya

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Fulawa cup 4
  2. Butter rabin leda
  3. Gishiri rabin chikali
  4. Sukari chokali biyu
  5. Madara chokali biyu
  6. Sai ruwa kofi daya
  7. Vanilla flavor chokali daya
  8. Abubuwanda muke bukata wurin yin source din kifin
  9. Kifi sukumbiya guda daya
  10. Attarugu
  11. Albasa
  12. Tafarnuwa
  13. Citta
  14. Maggi
  15. Curry da thyme
  16. Mai kadan
  17. Ganyen ugu ko alaiho ko lawashi

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zakitankade flour dinki kizuba a bowl sannan kisa gishiri sukari da madara ki jujjuya sannan kisa butter ki jujjuya sai kizuba ruwa kikwaba sosai sannan ki ajiye agefe

  2. 2

    Zaki wanke kifinki kisoyata sannan kibude kicire kayan duka sannan kidagargazashi

  3. 3

    Sai kidaura pan a wuta kisa mai chokali biyu sannan kiyanka albasa kanana kizuba akai kisoyata sama sama sai ki daka citta da tafarnuwa kizuba akai kijujjuya sai kisa jajjagen attarugu sannan kidauko kifin kizuba akai kijujjuya sai kisa kayan dandano da sinadaran kanshi kijuyashi sai kis ruwa chokali uku sannan kiyanka ganyenki kanana sannan kiwanke da gishiri sai kizuba akai kijuya sannan kibarta na minti hudu zuwa biyar sai kisauke

  4. 4

    Sannan kidauko kwabin flour din kirabata kashi hudu sannan kidau daya kimurzata da fadi sai kidauko hadin kifin kizuba akai sai kinadeta kamar nadin tabarma sai kidau wuka kiyankata sannan kishafa butter a bakin tire dinki sai kijerasu akai sannan kis a oven kigasashi

  5. 5
Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
rannar
Port Harcourt
Gskiya arayuwata inason girki sosai shiyasa kullum ina kicin wurin tsara abinci kalakala
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes