Farfesun naman rago

karima's Kitchen
karima's Kitchen @karima000100
Kano

Farfesu wani salo ne na musamman na sarrafa nama. Yana da saukin yi sannan kowa akwai yanda yake shirya nasa. A lokuta da dama ina yin farfesu don ya kasance abu ne wanda ba kowa ke son dafa shi ba. Don haka zaa ci shi da marmari.#NAMANSALLAH

Farfesun naman rago

Masu dafa abinci 8 suna shirin yin wannan

Farfesu wani salo ne na musamman na sarrafa nama. Yana da saukin yi sannan kowa akwai yanda yake shirya nasa. A lokuta da dama ina yin farfesu don ya kasance abu ne wanda ba kowa ke son dafa shi ba. Don haka zaa ci shi da marmari.#NAMANSALLAH

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

2hrs
biyu
  1. Kilo daya na naman rago
  2. Cokalikarami na curry powder
  3. Cokalikarami na thyme
  4. Cokalikarami na steak seasoning
  5. Cokalikarami na gishiri
  6. Cokalikarami na all purpose seasoning
  7. babba biyu na plain yoghurt Cokali
  8. Tarugu kanana guda goma
  9. Citta danya karami
  10. Albasa karama guda daya
  11. Ganyen naa naa babban cokali biyu
  12. Bay leaf guda daya
  13. Sinadarin dandano guda shida
  14. Man gyada cokali babba biyu
  15. Tafarnuwaguda shida

Umarnin dafa abinci

2hrs
  1. 1

    Ga hoton spices da nayi amfani dasu wajen hada wannan farfesun

  2. 2

    Ga sauran kayayyakin dana yi amfani dasu daga kan nama zuwa sauran kayayyakin.

  3. 3

    Zaa samu tukunya madaidaiciya a zuba naman a ciki sai a juye spices din. Maggi,gishiri,curry,thyme,bay leaf,steak seasoning da all purpose seasoning.

  4. 4

    Sai a raba albasan uku a yanka kashi daya a cikin naman. Sauran kashi biyun kuma a ajiye.

  5. 5

    Sai a sa ludayi a jujjuya sosai sinadaran dandanon su shige jikin naman sai ki zuba mai cokali biyu ki kara jujjuyawa.

  6. 6

    Sai a zuba ruwa daidai saman naman. Shi naman rago bashi da wahalan dahuwa sabida haka baa cika masa ruwa saidai in ana so a sami meat stock ne wato ruwan nama.zaa dafa naman tsawon mintuna talatin sannan a tsame a soya shi sama sama na tsawon mintuna goma a mai mai zafi

  7. 7

    Sai a dakko tukunyar da aka dafa naman a juye kayan da aka markada a zuba nama da aka soya sama sama a zuba ganyen naa naa akai a juya sai a maida akan wuta a dafa na tsawon awa guda.

  8. 8

    Tarugu,albasa,citta da tafarnuwa da na markada.

  9. 9

    Ga tukunya dana dafa nama da sauran ruwan nama a ciki

  10. 10

    Ga shi na hada nama da su tarugu da naa naa. Zan dora kan wutan.

  11. 11

    Zaa iya cin wannan farfesun da shinkafa.

  12. 12

    Zaa iya ci da pita bread

  13. 13

    Zaa iya cin sa da safe a matsayin breakfast,zaa iya ci da gurasa,alkubus ko funkaso.

  14. 14

    A wajen hada wannan girki mace zata iya amfani da duk kayan hadin da take da shi ba sai dole irin waanda nayi amfani dasu ba.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
karima's Kitchen
karima's Kitchen @karima000100
rannar
Kano

sharhai

Similar Recipes