Garau Garau

Ayshat Adamawa(U. Maduwa) @Ayshat_Maduwa65
Garau Garau abincin yan gayu ba😂 kafin nayi aure banason abincin nan amma yanzu na zama Oga akanshi. Agun wata kawata bahaushiya na faracin a lagos 😂 @Sams_Kitchen and @nafisatkitchen bismillan ku
Umarnin dafa abinci
- 1
Da farko Zaki daga wake idan ya kusan gama dafuwa Zaki wanke shinkafar ki d gishiri ki zuba ciki.
- 2
Idan ya dahu sai ki sauke.
- 3
Ki samo pan dinki ki zuba mai da albasan idan ta soyu sai ki sauke.
- 4
Ki wanke salak dinki da ruwa da gishiri sai ki yanka dasu cucumber da tumatir.
- 5
Sai ki samo plate ki jera yadda kikeson. Aci dadi lfy sai a kora da lemu mai sanyi. Zaki iya sa nama ko kifi
Yanayi
Wanda aka rubuta daga
Similar Recipes

Shinkafa da wake
#pantry. Abincin yan gayu wato garau garau kenan


Garau Garau
Garau garau ko shinkafa da wake abincine wanda yasamo asali ne daga arewacin nigeria,musamman kano,garau-garau yazama abincin na marmari da kuma abinci na sha awa,sbda yadda ake kayatashi abun zai baka sha awa wlh,to shine nima yau nace bari nayi muku garau-garau irin nawa ku biyoni domin ganin yadda nake kayata tawa shinkafar da wake💖amma fa karku manta kyan cin shinkafa da wake kacishi da sobo mai sanyi sanan a daki mai iska ko AC😂😂😂kana gama cii saika kwanta😂😂😂😂 #garaugaraucontest


Garau Garau
Garau Garau girkine na gargajiya Wanda muka gada tun iyaye da kakanni......garau garau abincine mai daukeda sinadarai masu gina jiki gakuma fadi dayake dashi....shiyasa naso na raba wannan kayataccen girki nawa na gargajiya (garau garau) daku.....bayan haka mahaifina ya kasance mason garau garau shisa nima nakesonta kunga kuwa abinda kakeso ka sowa Dan uwanka😘#garaugarauconteste


Shinkafa da wake (garau garau)
Garau garau abincin hausawa ne musamman wadanda suke a kano. Ina mutukar son garau garau domin shine abincin dana fi so naci yana d dadi sosai.xaki iya cinta da mai d yaji ko miya #garaugaraucontest#


Garau garau
#garaugaraucontest.garau garau abinci ne da asalinshi yazo daga wurin hausawa. Kusan kowa yanasonta maza da mata.


Garau garau daga Zara's delight
Garau garau (shinkafa da wake) abinchi ne wanda baa gajiya dashi kuma akafi amfani dashi a kowanne gida na hausawa musamman kanawa


Shinkafa da wake(garau-garau)
#garaugaraucontest. shinkafa da wake abincin hausawane mae dadi da farin jini,gashi kowa nasonsa,abincine da baa kashe kudi da yawa gurin yinsa amma sae dadi,ni bana wuce tayin garau-garau koda na koshi😂😂


Garau garau
#garaugaraucontest ina Mata masu matsalar dawuwar wake ga wata hanya da xaki dafa garau garau dinki Kiji y dahu yyi Lubus ba Tare d kinyi amfani d kanwa b


Garau garau
garau garau abincin gargajiya ne amma yanzu zamani yazo da ake kara masa wasu sina darai da zasu kara masa dadi kamansu cabeji,caras, kokumba,kifi da dai sauran su #garaugaraucontest


Shinkafa da wake (garau garau)
Shinkafa da wake itama tana daya daga cikin abincin gargajiya na hausawa. Shinkafa da wake tana da dadi musammanma idan taji mai da yaji mai dadi.


Garau Garau
Garau Garau abincine da yayi suna musamman ga nahiyar hausawa ,garau garau yana samuwa ne ta hanyar hada shinkafa da wake ,abinci ne mai gina jiki da kara lafiya musamman in an kawata shi da kayan lambu ire iren tumatir da dogon gurji da sauransu,ga saukin dafawa ga kuma gamsawar wa ga wanda yaci! Akwai hanyoyi da dabaru kala kala da ake amfani dasu wajen girka wake da shinkafa wato garau garau ,ni ga yadda nake dafa nawa !


Garau garau
#skg


Shinkafa da wake(garau-garau)
Shinkafa da wake abincin hausawane mae farin jini sosae,gashi baa kashe wasu kudi masu yawa gurin yinsa amma sae dadi,duk jumaa sae naci garau-garau 😂😍😋#garaugaraucontest


Shinkafa da wake(garau garau)
Yauma na sake dawowa da garau garau amma da farin wake wannan karan #garaugaraucontest


Garau garau mai fiya
Mai gidan yana son garau garau don haka na ke sarrafashi ta hanyoyi daban daban yanda bazai zama kullum kamar abu daya ake ci ba.


Garau garau
Garau garau abincin rana a kasar Hausa, musamman ma idan taji kayan hadi irin haka, baa bawa yaro mai kyuya. Garau garau tana da farin jini wajen al’umma, Ga saukin dafawa, ga dadi a baki, ga kara lafiya, ga kuma sa koshi. #garaugaraucontest


Garau garau
Mutane dayawa suna san garau garau, shiyasa nima nakeyawan yinta agidana sabida munajin dadin chinta nida iyalina. ban mantaba a amakranta muna kiranta barbadation sabida komai nata daga baya ake barbadawa sann aci, (maggi yaji da mangyada). sannan ataryyar nageria kawana sunfi kowa san gara garau, nazauna dasu na tsawon shekaru shidda shiyasa nina nake qaunarta. #Garaugaraucontest


Garau garau
Garau garau abinci ne da yayi suna musamman arewacin kasannan, ana yin garau garau ta hanyan shinkafa,wake da gishiri, amma yanzu da zamani yazo ana kara masa kayan lambu kaman su latas,latas,kokumba da dai sauransu..kuma abinci ne me kara lafiya balle wake yanzu zan nuna maku yanda nake garau garau dina#garaugaraucontest


Garau garau
Garau garau Dan dadi. #1post1hope


Garau garau girki daga mumeena’s kitchen
#garaugaraucontest Itadai garau garau wato shinkafa d wake abinchi Mai matukar farin juni ga mutanen Hausa musamman taji ganye ka hada d yajinka Mai dadi abinchi ne mai Sanya kuxari d Gina jiki habawa ba'a bawa yaro Mai kiya Yan uwa ga hanya mafi sauki wajen dafa garau garau kuma ki ganta fara Shar muje xuwa


Garau garau
#garaugarau contest abincin hausawa mafi soyuwa a zuciyar mutane


Garau garau shinkafa da wake
#pantry


Garau garau (shinkafar da wake)
Zan Iya kin cin komai amma banda garau garau, zan Iya cinta awa ishirin da hudu. Ga dadi ga amfani a jikin mutum#garaugaraucontest


Garau garau
#garaugaraucontest


Shinkafa da wake(garau garau)
Khady Dharuna #garaugaraucontest Garau garau tana daya daga cikin abincin hausawa da akafi so, wasu don kwadayi sukeyi Wanda mafi yawa anfiyi don abincin yau da kullum. Haka zalika yarana Suna sonta sosai...


Garau-garau
Nida iyalina muna son garau-garau kuma bama gajiya da ita shi yasa kullum burina in sarrafata a zamanance


Garau garau
Ayau inaso innuna asalin yanda ake garau garau Wanda kakan ninmu keyi kafin,kuma lokacin da shi akeyi kafin azo da abun a zama nance bari in tuno maku baya#garaugaraucontest


Shinkafa da wake
garau garau akwai dadi ba kadan ba


Shinkafa da mai da yaji
Fara da mai abincin ganta🤣😂 amma idan yaji veggies ba laifi akwai dadi#kanostate#teamkano


Shinkafa da wake garau garau
#hauwa inason garau garau sosae

More Recommended Recipes
https://cookpad.wasmer.app/ng-ha/recipes/15442991
sharhai (21)