Shinkafa dafaduka da coleslaw

_aisuph
_aisuph @aisuph
Nigeria
Tura

Kayan aiki

hr 1 da min 40mintuna
4 yawan abinchi
  1. Shinkafa
  2. Man gyada
  3. Tumatir,tarugu
  4. Sinadarin dandano
  5. Albasa mai lawashi
  6. Gishiri
  7. Kifi gasashe
  8. Cabbage, carrot da mayonnaise
  9. Ruwa
  10. Curry

Umarnin dafa abinci

hr 1 da min 40mintuna
  1. 1

    Ki iza tukunya a wuta sai ki zubw man gyada yayi zafi,ki zuba nikakken kayan miya da albasa sai kina juyawa har ya soyu,kisaka sunadarin dandano,curry kina juya har kayan miyan ya soyu sai ki tsaida ruwan dafa shinkafar ki ki rufe su tafasa.

  2. 2

    Ki wanke gasashen kifin ki da gishiri da ruwan gumi saboda idan akwai kasa a jiki duk zai fita,sai k dauraye da ruwan sanyi.
    Lokacin ki wanke shinkafar ki,idan ruwan ki na dahuwar ya tafasa,ki zuba shinkafar ciki sai ki zuba kifin ki kisa gishiri sai ki rufe ta dahu.

  3. 3

    Lokacin da ta dahu,,sai kisaka lawashin albasa ki kashe wutar girkinki ki rufe zafin dahuwar ya turara lawashin sai ki sauke ki juya shinkafar sbd lawashin yabi ko ina.

  4. 4

    Hadin coleslaw Kuma cabbage Zaki yanka sai kiyi grating carrot ki saka mayonnaise ki hade. Shikenan.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
_aisuph
_aisuph @aisuph
rannar
Nigeria
I love cooking because it is a state of flavors,balanced and blends of sweetness 😋.
Kara karantawa

Similar Recipes