Gurasar tanderu

Rukayya Jarma
Rukayya Jarma @ruky14744

Inason gurasa shiyasa da naga wannan na gwada yinta

Gurasar tanderu

Inason gurasa shiyasa da naga wannan na gwada yinta

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

mutum bakwai
  1. Kofi biyar Filawa
  2. Ruwa
  3. Gishiri kadan
  4. 1tbspoon Yeast
  5. Rabin tea spoon Baking powder
  6. Kofi Daya Mai

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ki tankade filawarki ki zuba yeast da gishiri kadan ki kwaba da ruwa yafi na wainar filawa kauri,ki rufe ki Kai rana awa Daya ko awa Daya da rabi

  2. 2

    Saiki dauko ki zuba baking powder itama kadan saiki sake kwabawa idan kinason albasa ki yanka a ciki

  3. 3

    Ki Dora kasko a wuta ki zuba Mai a ciki kina dauko kwabin kina zubawa in kasan yayi ki juya.

  4. 4

    Ki daka kuli kulinki da Maggi, gishiri,citta,barkono.ki yanka albasa tumatur, cabbage ko salat

  5. 5

    Ki zuba gurasar a plate ki barbada kuli kulinki a Kai ki zuba Mai akai saiki kawo hadin salat ki zuba

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Rukayya Jarma
Rukayya Jarma @ruky14744
rannar
Ina kaunar girki musamman snacks da Kuma Miya kala kala
Kara karantawa

sharhai (3)

Jamila Ibrahim Tunau
Jamila Ibrahim Tunau @Jamitunau
In zo muchi, Abinchin gargajiya akwai dadi :yum:

Similar Recipes