Dafadikar shinkafa

Fatima Bint Galadima
Fatima Bint Galadima @Homechef2000
Kano State

#sahurrecipecontest dafadikar shinkafa na daya daga cikin abinda iyalina sukeso saboda dadinta inason yinta da sahur saboda dadinta da saukin sarrafawa ku gwada zakuji dadinta

Dafadikar shinkafa

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan

#sahurrecipecontest dafadikar shinkafa na daya daga cikin abinda iyalina sukeso saboda dadinta inason yinta da sahur saboda dadinta da saukin sarrafawa ku gwada zakuji dadinta

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

mutum uku
  1. Shinkafa Kofi biyu
  2. Sinadarin dandano guda biyar
  3. cokaliGishiri rabin karamin
  4. Albasa guda biyu
  5. Attaruhu guda biyar
  6. Koran tattasai guda hudu
  7. Man gyada rabin kofi

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ga Kayan da nake buqata

  2. 2

    Ki dora shinkafa a wuta idan ta tafasa sae ki tace ta ki wanketa ki wanke Kayan miyanki ki jajjaga attaruhu,ki yanka albasa,ki yanka Koran tattasai

  3. 3

    Ki wanke namanki ki dora a wuta ki tafasashi da albasa da Kayan qamshi

  4. 4

    Idan Naman ya tafasa ki zuba attaruhu,albasa,man gyada, sinadarin dandano,gishiri ki soyasu idan ya soyu sae ki zuba ruwa Kofi daya idan ya tafasa ki zuba shinkafar ki ki zuba Koran tattasai sae ki juya ki rufe idan ya tso tse sae ki sauke

  5. 5

    Dafadikar shinkafa ta kammala ayi sahur lafiya da walwala😋😋

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Fatima Bint Galadima
Fatima Bint Galadima @Homechef2000
rannar
Kano State
I love cooking infact cooking is mah hobby I can spend all the day in kitchen without worrying my kitchen my pride!!!
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes