Tura

Kayan aiki

1hr 30 mint
3 yawan abinchi
  1. Kaza guda daya,ruwan khal cokali hudu babba
  2. Attaruhu guda takwas,Tattasai guda uku matsakaita
  3. Albasa babba guda daya,citta guda daya matsakaiciya
  4. Kanunfari kamar guda goma,masoro guda goma,Tafarnuwa biyu matsak
  5. Sai daddawa guda biyu matsakaita,sai mai dandano guda goma

Umarnin dafa abinci

1hr 30 mint
  1. 1

    Da farko yanka kazata yanda nakeson ta kasance sai na wanke ta na zuba ruwan khal akanta na sake zuba ruwa na wanke ta sosai saboda karni

    Sannan na dakko tukunyar da zanyi farfesu na a ciki na zuba kaza ta,na yanka albasa ta manyan yanka na zuba akan kazata

  2. 2

    Na dora akan wuta,sai na dakko citta kanunfari masoro da daddawa na daka a turmi sannan n zuba akan kazata,sai na zuba ruwa daedae Wanda zai dafa farfesu na har na samu romo a wadace saboda romo Yana da amfani a jikin mutum musamman na farfesun kaza

  3. 3

    Daga nan saina rufe kaza ta wacce tuni ta fara dahuwa,sannan na wanke attaruhu na da tattasai na jajjaga su na zuba su akan kaza ta na dakko mai dandano na na zuba na juya su komi ya ratsa cikin kazar nan sannan na rufe na rage wuta na bata lokaci har ta dahu

  4. 4

    Shikenan farfesun kaza ta ya kamma sai ci kawai,kuyi kokari ku gwada wannan hadin farfesun nawa yana da dadi sosai, ina muku fan alkhairi da fatan zamuci gaba da huwa cikin farin ciki.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Hygienic Snacks and Spices kn
rannar
I love cooking and making snacks
Kara karantawa

Similar Recipes