Kayan aiki

  1. 1Gyada kofi
  2. Ganyen zogala
  3. Nama
  4. Hadin kayan miya
  5. 6Dandano
  6. Mai cokali 3
  7. Daddawa kadan

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki murje gyada ki fece ta ki daka

  2. 2

    Ki dora mai a wuta ki yanka albasa ki zuba nikan kayan miya ki barsu su soyu

  3. 3

    Ki zuba ruwan nama a cikin tukunya ki kawo dunkulen dandano da daddawa ki zuba

  4. 4

    Ki wanke zogala ki zuba ki rufe tukunya

  5. 5

    Bayan minti goma se ki bude tukunya ki zuba dakakkar gyada ki juya ki rufe

  6. 6

    In ta dahu ki sauke za’a iya ci da kowane irin tuwo

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Hauwa Rilwan
Hauwa Rilwan @hauwaskitchen
rannar
Sokoto
I love cooking though I'm not perfect but trying to be
Kara karantawa

Similar Recipes