Kayan aiki

  1. 2Fulawa kofi
  2. Yeast cokali 1
  3. Gishiri
  4. Mai
  5. Yajin kuli

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ki tankade fulawa ki zuba yeast da gishiri a ciki ki kwaba da ruwa kar yayi kauri kuma kar yayi ruwa kamar dai kwabin fanke

  2. 2

    Rufe hadin a barshi ya tashi tsawon minti 20

  3. 3

    Idan hadin ya tashi se ki dora pan a wuta ki shafa mai ki debi hadin kina zubawa girman da kike so

  4. 4

    Idan ya gasu ki juya dayan barin shima har ya gasu

  5. 5

    Ki zuba mai da kuli ki kuma zaki iya yanka albasa da cabbage da tumatur in kina so

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Hauwa Rilwan
Hauwa Rilwan @hauwaskitchen
rannar
Sokoto
I love cooking though I'm not perfect but trying to be
Kara karantawa

Similar Recipes