Gurasa bandashe

Sam's Kitchen
Sam's Kitchen @Sams_Kitchen
Yobe State

Nayi wannan gurasar ne da niyya zanyi baking dinta amma dayake nidin 'yar nigeria ce😂😂 kuma gashi oven dina electric one ne bayan n gama komai sauran baking kawai sai sukamin halin nasu ( Nepa ) 😥😥shine sai nabi wannan hanyar na gasa gurasata kuma alhmdllh komai yayi tayi dadi sosai just give it try😋😋

Gurasa bandashe

Nayi wannan gurasar ne da niyya zanyi baking dinta amma dayake nidin 'yar nigeria ce😂😂 kuma gashi oven dina electric one ne bayan n gama komai sauran baking kawai sai sukamin halin nasu ( Nepa ) 😥😥shine sai nabi wannan hanyar na gasa gurasata kuma alhmdllh komai yayi tayi dadi sosai just give it try😋😋

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. 2 cupsFlour
  2. 1/2 tspGishiri
  3. Yeast ½ tbp
  4. 1 cupRuwa mai dumi
  5. Cabbage
  6. Ganyen albasa
  7. Carrot
  8. Mai
  9. Albasa
  10. Yajin kuli
  11. Yajin barkono

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ga abubuwanda muke bukata wajen yin gurasa 2 cups flour, ruwa 1 cup amma karki juyeshi duka zaki rage kamar 2 tbp, ½ tsp gishiri, ½ tbp yeast

  2. 2

    Zaki zuba gishiri,yeast ki gauraya saiki zuba ruwa ki juya sosai sai y zama dough

  3. 3

    Bayan kin gama zaki ajiyeshi wuri mai dumi ko ki kunna oven idan yayi zafi saiki kashe ki saka dough dinki a ciki ki barshi y tashi gashi nan bayan y tashi

  4. 4

    Saiki yayyanka dough dinki zuwa gida shida ki dauki guda daya ki fadadashi saiki shafa mai kadan a frying pan dinki saiki saka akai ki daura akan wuta ki gasa shi idan bangare daya yayi saiki juya zuwa dayan

  5. 5

    Hk zakiyi har ki kammala ga gurasar mu nan mun kammala saiki kuma muyi mata hadi

  6. 6

    Zaki fara saka yajin kulinki ki saka barkono (bansa barkono a cikin kuli naba shiyasa na saka ynz) ki saka mai ki saka cabbage dinki ganyen albasarki, carrot kadan d kuma albasa wanda kika yanka

  7. 7

    Sannan saiki yayyanka gurasarki kanana ki kara mai maita mata abunda kk yi a farko shknn saici

  8. 8
  9. 9
Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Sam's Kitchen
Sam's Kitchen @Sams_Kitchen
rannar
Yobe State
Cooking is my favorite
Kara karantawa

Similar Recipes