Bandashen gurasa

Umm Muhseen's kitchen
Umm Muhseen's kitchen @cook_20400043
Yobe State

A gsky naji dadin wannn bandashe sosai kuma iyalai n sunyi farin ciki sosai sunji dadin shi

Bandashen gurasa

Masu dafa abinci 100+ sun ziyarci wannan girkin

A gsky naji dadin wannn bandashe sosai kuma iyalai n sunyi farin ciki sosai sunji dadin shi

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Fulawa
  2. Yis
  3. Dakakken kuli
  4. Albasa
  5. Tumatiri
  6. Yajin barkono
  7. Man gyada
  8. Sinadarin dandano
  9. Kabeji

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki tanadi fulawa ki tankade ta saiki zuba yis ki gauraya saiki zuba ruwa ki kwaba bada kauri ba saiki saka a rana domin y tashi idan y tashi

  2. 2

    Saiki wanke marfin tukunya ki shafa toka a bayan marfun tukunya saiki daura akan wuta idan y dauki zafi sosai saiki zuba mai kadan shafawa zakiyi kawai saiki zuba kullin gurasar taki idan y soyu saiki juya zuwa dayan gefen Shima yayi hk zaki tayi har ki kammala amma idan kin saka mai sau daya saiki guda biyar ma baki kara zubawa ba

  3. 3

    Idan kin kammala saiki dakko wani kwano ki zuba a ciki ki zuba mai gyada, garin kuli, yajin barkono, sinadarin dandano, ki yanka albasa da tumatur da kabeji ki zuba saiki gauraya ki dan dana idan komai yaji shknn kin kammala bandashen gurasar ki saiki zuba a plate aci da iyalai kuyi girki cikin farin ciki d annashuwa 😋

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Umm Muhseen's kitchen
rannar
Yobe State
cooking is my favorite 😋
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes