Kayan aiki

  1. Fulawa kofi takwas
  2. Ruwa kofi biyu ko fiye
  3. Yeast 1tbsp+1tsp
  4. Madarar gari rabin kofi
  5. Mai bada yawa ba
  6. Sugar kofi daya
  7. Kwai daya babba
  8. Gishiri bada yawa ba

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki tanadi kayan hadin ki kamar haka

  2. 2

    Sae ki tankade fulawar ki a cikin roba,ki barbada gishiri kadan ki zuba madara sannan ki yamutse su

  3. 3

    Ki zuba mai bada yawa ba,ki murza fulawar da hannun ki sai ke tabbata baki jin kolallai

  4. 4

    Sannan ki jika yeast cikin ruwa masu dumi idan yana da kyau zaki ga yana kumfa y kumburo sae ki zuba kwai da sugar ki yamutse ta har ta narke,sannan ki zuba cikin hadin fulawar ki ki yamutsa ki kwaba ta sosai har sae ta kwabu,sannan ki rufe ki barshi ya tashi

  5. 5

    Idan ya tashi sae ki mulmula shi girman yadda ki kike so,nidae shape biyu nayi,normal doughnuts da ring doughnuts sae ki barbada fulawa akan tray ki aza doughnut dinki ki aza wurin da keda rana

  6. 6

    Idan ya kumbura sae ki aza Mai a wuta ki soka yatsar ki idan kinji y fara zafi sae ki sa doughnuts dinki idan kasa ya fara soyuwa sae ki juya dayan gefen ya soyu shima.sannan doughnuts ba'a cika mai wuta

  7. 7

Yanayi

Gyara girkin
See report
Tura

sharhai

Wanda aka rubuta daga

Hauwa'u Aliyu Danyaya
rannar
Sokoto
I love cookingcooking is my fav😍❤️
Kara karantawa

Similar Recipes

More Recommended Recipes