Bredi mai nikakken nama aciki

TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA) @cook_15480513
Port Harcourt

Wato nalura idan kanason kaci brodi mai dadi kuma mai laushi toh kar kabata kudinka wurin siyanta a kasuwa. Kayi kokari kayishi agida shi yafi dadi wlh#BAKEBREAD

Bredi mai nikakken nama aciki

Masu dafa abinci 3 suna shirin yin wannan

Wato nalura idan kanason kaci brodi mai dadi kuma mai laushi toh kar kabata kudinka wurin siyanta a kasuwa. Kayi kokari kayishi agida shi yafi dadi wlh#BAKEBREAD

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Flour kofi uku
  2. Butter chokali babba biyu
  3. Yeast chokali babba daya
  4. chokaliBaking powder rabin
  5. Sugar chokali daya
  6. Kwai daya
  7. chokaliMilk flebo rabin
  8. Madarar gari chokali daya
  9. chokaliVanilla flavor na gari rabin
  10. Ruwan dumin rabin kofi
  11. Kayan hadin ciki
  12. Nikakken nama
  13. Albasa
  14. Curry
  15. Attarugu
  16. Mai
  17. Maggi dunkule kwaya biyu

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Dafarko natankade fulawa nazuba aroba sai nazuba sugar madara baking powder da yeast da milk powder da garin flabo najujjuya sai nazuba kwai sannan nazuba na kwabashi sai nakawo bota nazuba nasake kwabawa dakyau. Kafin yatashi sai kihada naman da zakisa aciki. Dafarko nadaura pan a wuta nasa mai sai nazuba nikakken nama nayi ta juyawa harsawon minti biyu sai nazuba albasa da attarugu tareda maggi da curry najujjuya sai nazuba ruwa kadan nabarta yadahu dakyau har yashanye ruwan sai nasauke

  2. 2

    Sai nadauko fulawa ta da nakwaba nasake bugawa dakyau sai nararrabata sai nadau daya bayan daya ina murzata da fadi dakuma tsayi sai nadau naman nazuba akai sai nanannadeta nasaka acikin pan dina da nariga da nashafa butter aciki. Haka nayiwa duka. Sai nasake barinta zuwa minti goma sbd yatashi bayan yatashi sai nashafeta da narkakken butter sai nasa a oven nagasata

  3. 3
  4. 4
  5. 5
Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
rannar
Port Harcourt
Gskiya arayuwata inason girki sosai shiyasa kullum ina kicin wurin tsara abinci kalakala
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes