African jallof rice

Masu dafa abinci 100+ sun ziyarci wannan girkin
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Shinkafa
  2. Man jaa
  3. Tarugu
  4. Tattasai
  5. Albasa
  6. Kayan qamshi
  7. Dandano
  8. Busashshen kifi
  9. Ruwa
  10. Naana(domin qawata abincin)

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki fara gyara tarugu,tattasai da Albasa sai ki barzasu a blender ko ki daka

  2. 2

    Sae ki zuba man jaa acikin tsaftataccen tukunya sae ki kada mai Albasa kadan in ya fara kanshi sai ki kawo barzonki sai ki zuba,ki Kila dashi kina motsawa har ya soyu

  3. 3

    Sai ki zuba ruwa kwatanci,ki zuba Dandano da kayan qamshi sae ki rufe

    Sae ki dauko busashshen kifinki ki zubamai ruwan zafi ki wankeshi da kyau datti ya fitaki cire qayanshi ki sai ki zuba a tukunyanki ki rufe

  4. 4

    Idan tukunyanki ta tafasa sai ki wanke shinkafarki(ki zuba mata ruwa ki murzata dattin ya fita sae zubarda wannan ruwan ki canja wani ki sake murzata ki tsiyaye ruwan)sae ki zuba acikin tafasasshshiyar tukunyanki sae ki motse ki rufe

  5. 5

    Idan ta tsane sae a sauke azuba a mazubi,sai ki saka naana domin qawata abincinki

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
hafsat wasagu
hafsat wasagu @Wasagu03
rannar
Sokoto
Food loverchemist
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes