Dafadukan shinkafa da hadin kayan lanbu

salma sulaiman
salma sulaiman @cook_16696007

Dafadukan shinkafa da hadin kayan lanbu

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Shinkafa
  2. Tumatur
  3. Albasa
  4. Attaruhu
  5. Maggi
  6. Cabeji
  7. Karas
  8. Kokumba
  9. Kwai
  10. Man salak
  11. Gishiri

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    A wanke kayan miya sai a jajjagasu a zuba mai a cikin tukunya idan yayi zafi sai a zuba jajjagen a soyasu a zuba maggi gishiri curry a agauraya sai a kara ruwa a rufe tukunyar a barshi ya tafasa sai a wanke shinkafa a zuba a cikin ruwan tukunyar a rufe ba barta ta dahu sannan a sauke

  2. 2

    Awanke karas kabeji kokumba a yayyanka su sai a hada su a roba a zuba man salak akai a gauraya

  3. 3

    A dafa kwai a bare a aje agefe

  4. 4

    A danyi jajjagen kayan miya kadan sai a zuba mai a kasco kadan idan yayi zafi sai a zuba jajjagen a soyasu a zuba maggi curry ya yanka dafaffan kwai a saka a gauraya sai a sauke.zaa sami faranti a zuba shinkafar sai a zuba hadin kabeji sannan a zuba jajjagen a sama sai a jera yankakken kokumba agefe.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
salma sulaiman
salma sulaiman @cook_16696007
rannar

sharhai

Similar Recipes