Hadin kunu na mata(Gyara da kanki)

Jahun's Delicacies
Jahun's Delicacies @4321ss
Kano,Danladi Nasidi Estate.

Wannan kunu sadaukarwa ne ga Dukkan mata, dan Amfaninsa yana da yawa.

Hadin kunu na mata(Gyara da kanki)

Wannan kunu sadaukarwa ne ga Dukkan mata, dan Amfaninsa yana da yawa.

Edit recipe
See report
Share
Share

Ingredients

  1. Farar shinkafar tuwo- Gwangwani-daya
  2. Alkama-Gwangwani-daya
  3. Gyada-Rabin-gwangwani
  4. Aya-Rabin-gwangwani
  5. Hulba-Daya bisa hudu na gwangwani
  6. Dabino-Gwangwani-daya
  7. Waken Soya- rabin-gwangwani
  8. Kayan hadi
  9. Madara ta ruwa
  10. Mazarkwaila/Sugar

Cooking Instructions

  1. 1

    Zaki auna gwangwani daya na farar shinkafarki ki wanke tas ki shanya ta bushe.

  2. 2

    Itama alkama zaki auna gwangwani daya ki tsince tsakuwa, ki fitar da datti, ki wanke ki shanya ta bushe.

  3. 3

    Gyadar ma zaki auna rabin gwangwani, ki zuba a frying pan ki soya sama sama dan ta bushe kuma wanan bawon zai yi saurin fita(idan kin tashi soyawar babu mai babu ruwa, kai tsaye zaki zuba a frying pan ki rage wuta kiyi ta juyawa) idan kin sauke kisa hannanenki ki murtsuke zaki ga brown bayan ya fita cikin sauki, kuma gyadar zata bushe babu maikon mai.

  4. 4

    Aya rabin gwangwani zaki regeta kuma ki wanke tas dan akwai qasa sosai a jikinta da tsakuwa, itama bayan kin wanke ki shanya ta bushe.

  5. 5

    Dabino busashe, idan kin sayi wanda bai gama bushewa ba to ki bare shi, ki cire kwallon ki shanya ya bushe sosai.

  6. 6

    Hulba ba'a bukatar ta da yawa dan ita tana da karfi, idan tayi yawa bazaki ji dadin kunun ba, gashi kuma tafi ragowar kayan hadin tasiri a jiki. Zaki auna 1/4 gwangwani ki ajiye.

  7. 7

    Waken soya, zaki auna rabin gwangwani ki bayar a nika ya zama gari.

  8. 8

    Dukkan wadanan hayan dana lissafo zaki hada su waje daya ki bayar a niqo miki su zama gari, sai ki ringa diban chokali 3 babban cokali ki dama da ruwan sanyi ki ajiye, sai ki zuba kamar kofi daya na ruwa a wuta ya tafaso, sai ki juye wanan hadin da kika dama a tukunyar kina juyawa, har sai kinga yayi kauri, ki rage wuta ki bashi minti 4 kina tsaye ki kashe.

  9. 9

    Ki hada da madarar ruwa ki sha.

  10. 10

    Zaki saka sugar ko mazarkwaila dai dai da dandanon da kike so.

  11. 11

    Zaki ringa shan wanan kunu sau 2 a rana, safe da yamma.

    1-Mace mai shayarwa da take shirin yaye, sai ta fara sha sati daya kafin yaye har zuwa sati biyu bayan yaye.

    2-Mace mai son kiba da murmurewa zata sha sau biyu a rana har tsawon sati 2 ko izuwa yanda taga jikinta yayi.

    3-Amarya da uwar gida duk zasu iya amfani da shi, a sha safe da yamma har kwana 7.

    4-Mace mai neman cikowar kirjinta zata hada da garin agada(plantain) a niko tare da ragowar kayan hadin, ta ringa sha tsawon sati 2.

Edit recipe
See report
Share
Cook Today
Jahun's Delicacies
on
Kano,Danladi Nasidi Estate.
Sadiya Salisu Jahun,was born and brought up in kano,an Msc.holder on Agricultural Extension,i love cooking and i think to be a great chef you have to be a great teacher, i love doing classes with people who loves and enjoy food,bringing them all around one table to speak.
Read more

Comments

Naazy_
Naazy_ @naazy_
Mungode kwarai. Zan iya amfani da powdered hulba din? Kuma shima still quarter zanyi using ko measurement din zey canja?

Similar Recipes