Shinkafa da wake da mai da yaji

Elteemahzcakesndmore
Elteemahzcakesndmore @cook_14837175
Kano,Nigeria

Shinkafa da wake da mai da yaji ya samu asali ne daga gidajen marasa karfi inda suke dafawa su sa mai da yaji suci. Masu hali ke kiranta da GARAUGARAU domin a ganinsu abincin da ba nama koh kifi ya zama garaugarau.Garaugarau ya samu karbuwa sosai awajen jama'a domin mutanen dayawa ya zamto musu abinci mafi soyuwa don basa gajiya da cin sa. Ana sarrafa wannan abinci ta hanyar dafa shinkafa da wake a tukunya guda a sa mai da yaji a ci. A na cinsa da man kuli koh manja...idan da hali akan yanka ganyen salak,tumatir da albasa a ci da ita....karbuwar da ya samu ne yasa ake kawata shi yanzu da abubuwa iri iri (kaza,naman kasuwa, soyayyen kifi, kwai,hadadden salad da sauransu) #garaugaraucontest

Shinkafa da wake da mai da yaji

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan

Shinkafa da wake da mai da yaji ya samu asali ne daga gidajen marasa karfi inda suke dafawa su sa mai da yaji suci. Masu hali ke kiranta da GARAUGARAU domin a ganinsu abincin da ba nama koh kifi ya zama garaugarau.Garaugarau ya samu karbuwa sosai awajen jama'a domin mutanen dayawa ya zamto musu abinci mafi soyuwa don basa gajiya da cin sa. Ana sarrafa wannan abinci ta hanyar dafa shinkafa da wake a tukunya guda a sa mai da yaji a ci. A na cinsa da man kuli koh manja...idan da hali akan yanka ganyen salak,tumatir da albasa a ci da ita....karbuwar da ya samu ne yasa ake kawata shi yanzu da abubuwa iri iri (kaza,naman kasuwa, soyayyen kifi, kwai,hadadden salad da sauransu) #garaugaraucontest

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Wake
  2. Shinkafa
  3. Man kuli
  4. Yankakkeyar albasa
  5. Haddadden yajin barkono
  6. Dunkule
  7. Gishiri

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Za a auna wake a tsince Mara kyau a ajiye a gefe...a auna shinkafa itama a jiye a gefe (ya danganta da adadin masu cin abincin) ana so shinkafar ta rinjayi waken

  2. 2

    A zuba ruwa a tsabtataccen tukunya (Rabin tunkuyar) a daura a wuta ya tafaso

  3. 3

    Idan ruwa ya tafasa a wanke wake a zuba a cikin tafasashshen ruwan...a daidai wannan lokacin wasu na saka kanwa yar kadan don waken yayi saurin laushi...idan waken ki many a ne masu kyau kuma basai kinda kanwa ba idan aka yi haquri zai yi laushi cikin kankanin lokaci sai a rufe tukunya a barshi har sai ya dauko dahuwa

  4. 4

    Idan waken ya dauko dahuwa sai a wanke shinkafa a barta tayi tafasa biyu zuwa uku sai a juye a matsani

  5. 5

    A mai da tukunya kan wuta a zuba ruwa kadan da gishiri kadan a rufe ya tafaso

  6. 6

    A kwara wa shinkafa da waken dake matsani ruwa sosai abarta ta tsane idan ruwan ya tafasa sai a juye Shinkafa da waken a jujjuya sai a rufe har sai ya dahu ruwan jiki ya tsotse sai a sauke

  7. 7

    A daura kaskon suya a kan wuta a zuba man kuli idan yayi zafi a zuba yankakkiyar albasa a soya idan ta soyu a sauke a kashe wuta

  8. 8

    A samu mazubi mai kyau da tsabta a zuba dafaffiyar shinkafa da wake a sa mai a marmasa dunkule a barbadeta da yaji...aci dadiiii lafiyaaaaaaaaa

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Elteemahzcakesndmore
Elteemahzcakesndmore @cook_14837175
rannar
Kano,Nigeria
A Baker, an aspiring chef,..... Not your regular foodie.. Strong passion in cooking and food photography
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes