Fish cake

Masu dafa abinci 2 suna shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki wanke kifi da lemon tsami saiki saka cikin tukunya ki zuba ruwa dan dai-dai ki yanka albasa ki zuba ki saka maggi da gishiri da kayan k'amshi ki daura akan wuta ya dahu tsahon minti 10 saiki sauke ki cireshi daga cikin ruwan yasha iska.

  2. 2

    In yasha iska saiki cire kayoyin ki daka a turmi ki gyara albasa da attaruhu da tafarnuwa ki jajjaga ki zuba kan kifin ki fasa kwai ki kara maggi da d'an gishiri ki jujjuya saiki daura a leda ki saka acikin tukunya ki zuba ruwa ki daura kan wuta yayita dahuwa inya dahu zakiga duo ya task sama saiki sauke tukunyar ki ciccire kifin a cikin ruwan in yasha iska ki yage ledar ki saka wuka ki yayyanka fish cake d'in a kwakwkwance.

  3. 3

    Saiki zuba mai a kasko ki daura akan wuta ki fasa kwai ki yanka albasa kidan saka magi kadan sai kina saka kifinnan cikin ruwan kwai kina juyawa kina saka a cikin mai a haka harki gama inya soyu ki kwashe shikenan.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Umma Sisinmama
Umma Sisinmama @cook_14224461
rannar
Kano
I was born in kano state
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes